A cikin jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yayi a wurin taron bitar ayyukan da gwamnatin sa ta aiwatar wa ƴan Najeriya, shugaba Buhari ya ce an aiwatar da ayyuka masu tasiri a fadin kasar nan, wadanda suka cika buri da muradin ƴan Najeriya.
Wannan taro na musayin ra’ayoyi ne da kuma yin bitar ayyukan da gwamnati ta aiwatar a tsawon shekaru 7 a Najeriya wanda ministoci da shugabannin ma’aikatu za su tattauna akai.
Shugaba Buhari, ya ce ” Gwamnatin tarayya ta aiwatar da ayyuka masu yawan gaske a kasar nan musamman na raya kasa.
” Mun shimfiɗa sabbin hanyoyi a kasar nan masu tsawon kilomita 3,800 sannan kuma mun siyo sabbin jiragen saman yakin rundunar sojin saman Najeriya da za su iso Najeriya nan ba da daɗewa ba.
” Sannan kuma mun yi wa akalla mutum miliyan 38 rigakafin Korona wanda shima nasara ce da muka samu.
” Wasu daga cikin manyan nasarorin da aka samu sun hada da kammala aikin layin dogo mai tsawon kilomita 326 daga Itakpe-Ajaokuta-Warri da kuma Kammala aikin sabunta layin dogo na sama da kilomita 156.5 daga Legas zuwa Ibadan tare da fadada tashar jirgin ruwa ta Legas, Apapa.
“Akan ayyukan tituna, wannan gwamnatin ta gina tituna mai tsawon kilomita 408, da kuma titin SUKUK kilomita 2,499 da kula da tituna mai tsawon kilomita 15,961 a fadin kasar nan.
“ Wasu daga cikin muhimman ayyukan sun hada da gina gadar Neja mai nisan kilomita 1.9 da ta hada jihohin Anambra da Delta mai tsawon kilomita 10.30, gyara, ginawa da fadada titin mota biyu daga Legas zuwa Shagamu-Ibadan, aikin gyaran Abuja-Kaduna – Zaria – Kano, da sauransu.”
Discussion about this post