Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa gwamnatin sa a kan ƙoƙarin da sojojin Najeriya su ka yi wajen ceto ragowar fasinjojin jirgin ƙasa su 23 da ke hannun ‘yan bindiga.
A ranar Laraba ce gwamnatin tarayya ta bada sanarwar cewa sojojin Najeriya sun kuɓutar da ragowar fasinjojin su 23, bayan sun shafe kwanaki 192 a hannun ‘yan ta’adda.
Sanarwar ta ce an samu nasarar kuɓutar da su ne misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Laraba.
Sai dai kuma har yanzu ba a san yadda aka kuɓutar da su ɗin ba, sannan kuma ba a bayyana shin an kashe ‘yan ta’addar ne ko salum-alum aka kuɓutar da su.
Ragowar fasinjojin dai sun samu kuɓuta bayan sun shafe fiye da watanni shida a hannun ‘yan bindiga.
Kuɓutar da su ɗin da aka yi mako ɗaya bayan fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da kuma yadda Buhari ya jinjina wa gwamnatin sa kan ƙoƙarin da ya ce ta yi wajen kuɓutar da su, ya sa wasu na ganin cewa gwamnatin na so ta nuna wa ‘yan Najeriya cewa ta yi abin bajinta.
Buhari dai ya jinjina wa Sojojin Najeriya da sauran dukkan hukumomin tsaro. Kuma ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bayar da muhimmanci da fifiko wajen tsaron ƙasar nan.
A ranar 28 Ga Maris ce Boko Haram su ka kai wa jirgin mumnunan hari, bayan ya tashi daga Abuja, kan hanyar sa ta zuwa Kaduna.
An buɗe wa jirgin wuta, aka kashe mutum 8, kuma aka bayyana cewa an rasa inda fasinjoji 168 su ke.
Sai dai kuma daga baya aka tabbatar da cewa fiye da 60 a cikin su duk ‘yan ta’adda ne su ka yi garkuwa da su.
Tun daga ranar dai har yau zirga-zirgar jiragen ƙasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna da Kaduna zuwa Abuja, ta tsaya cak, babu ranar ci gaba, kuma babu lokaci.
Discussion about this post