Kotun majistare dake Ikeja a jihar Legas ta bada belin barawon Littafi Mai Tsarki wato ‘Bible’ hudu wanda farashinsu ya kai Naira 72,230 akan Naira 200,000.
Alkalin kotun H. B Mogaji ya yanke wa Godwin Idumu mazaunin lanba ta 9 Emmanuel layin Maryland wannan hukunci ranar a cikin farkon wannan mako.
Alkali Mohaji ya ce Idumu zai gabatar da shaida daya a zama na gaba da kotun za ta yi.
Ya ce za a ci gaba da shari’ar ranar 35 ga Nuwanba.
Lauyan da ta shigar da karan Felicia Okwori ta ce Idumu ya aikata satar ne a tsakanin ranar 4 ga Disemba 2021 da 3 ga Yuni 2022 a babban kantin Ebeano dake GRA a Legas.
Okwori ta ce a ranar 4 ga Disemba 2021 Idumu ya sace Littafi Mai Tsarki guda biyu daga wani kanti da farashinsu ya kai Naira 51,080.
A lokacin masu kantin sun ga lokacin da Idumu ke satar ‘Bible’ din a na’urar CCTV sai dai ya tsere kafin a kama shi.
Ya ce daga nan sai Idumu ya sake dawowa wannan kantin ranar 3 ga Yuni 2022 ya sake sace wasu guda biyu da farashin su ya yai Naira 22,150.
Okwori ta ce a wannan ranar dubun Idumu ya cika domin kafin ya gudu aka damke shi.
Sai dai kuma duk da hujjojin da aka gabatar Idumu ya karyata zargin ya ce bai aikata haka ba.
Discussion about this post