Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa ta soke rajistar mutum 2,780,756 daga miliyoyin waɗanda su ka yi rajistar mallakar katin rajistar zaɓen da aka kammala watannin baya (CVR).
Shugaban INEC ne Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a ranar Laraba, a lokacin taron ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa, a Abuja.
Tun da farko dai a baya an bayyana cewa mutum 12,298,944 ne su ka yi rajistar da aka kammala cikin Yuni zuwa Yuli, 2022.
Sai dai kuma Yakubu ya tabbatar da cewa an tsame sunayen masu rajista har su 2,780,756 daga cikin miliyan 12 ɗin, aka bayyana cewa duk ba a cika su daidai ba.
Ya ce dalilan cire sunayen sun haɗa da yin rajista sau biyu, ƙarancin shekarun wasu da su ka yi rajistar da sauran dalilai.
“A ƙarshen wa’adin yin rajistar dai an samu ‘yan Najeriya 12,298,944 su ka kammala yin rajistar su a matsayin su na sabbin masu rajista.
“Mun kuma sha cewa tsarin mu na tsaftacewa da share rumbun rajistar zaɓe mai inganci ne sosai.
“Bayan mun yi gagarimin tantancewa ta hanyar amfani da tsarin ƙeƙe-da-ƙeƙe (ABIS), an samu rajistar da ba ta cancanta ba har ta mutum 2,780,756.
“Yawancin su ta waɗanda su ka yi rajistar bogi ce, sai waɗanda su ka yi rajista sau biyu da kuma waɗanda su ka fara rajista, amma ba su cika sharuɗɗan tattabar yin rajistar mallakar katin zaɓe ba.
“Saboda haka a yanzu adadin yawan sabbin rajistar da aka yi su ne 9,518,188,” inji shugaban INEC.
Haka nan kuma ya ƙara da cewa nan gaba adadin yawan masu rajistar zai iya canjawa cikin kwanaki masu zuwa, yayin da aka bayyana sunayen a fili domin jama’a su bi diddigin da jama’a za su yi da kuma ƙorafe-ƙorafe kafin kwanaki 90 da zuwan ranar zaɓe,” inji Yakubu.
Discussion about this post