Ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya sun gargadin mutanen kasashen su da ke zaune a babban birnin tarayyar Najeriya da su kula matuka domin akwai yiwuwar yan ta’adda za su kawo hari babban birnin.
Amurka ta ce za ta rage lokuttan aiki a ofishin jakadancin ta dake Abuja.
Bisa ga sanarwar akwai yiwuwar ‘yan ta’adda za su kai hari wasu manyan gine-gine da ofisoshi, makarantu, gidajen abinci, wuraren shakatawa da dai wasu muhimman wurare da jama’a kan taro a Abuja.
Ita ma kasar Birtaniya ta fitar da sanarwa irin haka ga ‘yan kasan ta da ke Najeriya.
Idan ba a manta ba, Kasar Austrailia ta fitar da irin wannan sanarwa inda ta gargadi mutanenta da su kiyaye zuwa Najeriya domin tsananin rsahin tsaro da sace-sacen mutane da ake yi.
Sai dai kuma hukumar tsaron Najeriya ta fitar da sanarwar cewa ba abu bane da mutane za su tada hankulan su a akai.
Darektan hulda da Jama’a na hukumar Peter Afunanya, ya bayyana cewa hukumomin tsaron Na jeriya na sane da haka kuma suna kokarin ganin abu irin haka bai auku ba.
Ya ce ” Dama akwai irin wannan gargadi da ake fitar wa domin mutane su rika ankarewa.Abu daya da muke rokon jama’a shine su baiwa jami’an tsaro hadinkai da goyon baya wajen taimaka musu da bayanan sirri.”
A karshe ya hori mutane su gujewa kai kansu wuaren da babu cikakken tsaro sannan kuma a rika kiyayewa, amma jami’an tsaro na kan gaba akan haka.
Discussion about this post