Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana cewa matsawar Najeriya ba ta tashi tsaye ta daƙile barayin danyen mai da masu fasa bututu ba, to nan ba da daɗewa ba tattalin arzikin Najeriya zai iya durƙushewa.
Lawan ya yi wannan bayani lokacin da ya ke gabatar da jawabi kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya fara jawabin gabatar da Kasafin 2023 na naira tiriliyan 20.52 a Majalisar Tarayya.
Lawan ya ce a yanzu ɓarayin ɗanyen mai su ne manyan abokan gabar Najeriya. “Ya kamata a tashi haiƙan a kakkaɓe wannan gagarimar matsalar ta ɓarayin ɗanyen mai, kafin su kai ga tarwatsawa ko durƙusar da tattalin arzikin Najeriya.”
Lawan ya ce idan aka magance gagarimar satar ɗanyen mai, to za a samu ƙarin kuɗaɗen shiga, kuma hakan zai rage ciwo bashi, tare da rage giɓin kasafin kuɗi.
Shawara ta biyu da Sanata Lawan ya bayar, ita ce “a sake nazarin ɗage biyan harajin shigo da wasu kaya da ake yi wa wasu mutane ko kamfanoni. Kuma a rage bai wa wasu kamfanoni iznin karɓar haraji a madadin gwamnatin tarayya ana biyan su lada.
“Kuma a rage bai wa wasu kamfanoni damar kashe kuɗi su na yin wasu ayyukan gwamnatin tarayya, daga baya su na karɓar haraji har sai sun karɓi kuɗin kwangilar su da ribar su tukunna.”
Lawan ya buga misali da cewa hukumomi ne irin su Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, Hukumar NIMASA da Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), duk kamata ya yi su riƙa karɓar harajin su da kan su, kamar yadda Hukumar Kwastan da Hukumar Tara Kuɗaɗen Harajin Cikin Gida (FIRS) ke Karɓar na su da kan su, ba wasu kamfanoni ke karɓar masu ba.
Lawan ya ce waɗannan duk hanyoyi ne na ƙarin kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya, waɗanda za su haifar da rage ciwo bashi don a cike giɓi a kasafin kuɗi.
Sanata Lawan ya bayar da shawarar daƙile ɓaray in ɗanyen mai, mako guda bayan Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya ce an gano inda ɓarayin mai ke tace ɗanyen mai har wurare 395 a cikin makonni shida.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Buhari ya ce Za a ciwo bashin naira tiriliyan 8:8, don a cike giɓin Kasafin 2023.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar Kasafin 2023 na naira tiriliyan 20:51, a gaban Majalisar Tarayya.
Kasafin wanda ya gabatar a ranar Juma’a, shi ne na takwas kuma na ƙarshe a mulkin sa da ya gabatar.
A cikin jawabin sa, Buhari ya bayyana cewa za a samu giɓi na naira tiriliyan 10.78, amma kuma za a cike giɓin da kuɗaɗen bashin da za a ciwo har naira tiriliyan 8.8.
Haka nan kuma ya ce a cikin kasafin, za a kashe naira tiriliyan 6.31 wajen biyan basussuka.
Ya bayyana cewa an tsara kasafin bisa kintacen cewa Gwamantin Tarayya za ta samu kuɗin shiga har naira tiriliyan 16.87 cikin 2023. Kuma ana sa ran a riƙa haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 1.69 a kowace rana, yayin da aka yi kintacen cewa za a riƙa sayar da kowace ganga ɗaya kan Dalar Amurka 70.
Wannan kasafin wanda aka raɗa wa suna Kasafin Rage Giɓi Da Rage Ciwo Bashi, ya nuna bai ci sunan sa ba, domin za a ciwo har naira tiriliyan 8.80 a matsayin bashi cikin 2023.
Yayin jawabin sa, Buhari ya yi bitar ayyukan da gwamnatin sa ta gudanar cikin shekaru bakwai da kuma bibiyar yadda aka kashe kuɗaɗen kasafin 2022.
Discussion about this post