Duk da kukan ƙarancin kuɗaɗen shiga cikin aljihun gwamnati da kuma biyan basussukan da gwamnatin za ta yi a cikin 2023, hakan bai hana gwamnatin tarayya kasafta naira tiriliyan 1.1 don ta Kashe wajen wani ɓangare na ayyukan yau da kullum ba.
Kuɗaɗen dai za su tafi wajen gudanar da ayyukan gwamnati da su ka haɗa har da tafiye-tafiye da kuɗaɗen mai da gyaran jirage da sauran su.
Aƙalla gwamnatin Buhari ta yi ƙarin kashi 40% daga adadin kuɗaɗen da ta kashe wajen wannan ɓangaren ayyukan yau da kullum.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Gwamantin Buhari za ta ciwo bashin naira tiriliyan 8:8 a 2023.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar Kasafin 2023 na naira tiriliyan 20:51, a gaban Majalisar Tarayya.
Kasafin wanda ya gabatar a ranar Juma’a, shi ne na takwas kuma na ƙarshe a mulkin sa da ya gabatar.
A cikin jawabin sa, Buhari ya bayyana cewa za a samu giɓi na naira tiriliyan 10.78, amma kuma za a cike giɓin da kuɗaɗen bashin da za a ciwo har naira tiriliyan 8.8.
Haka nan kuma ya ce a cikin kasafin, za a kashe naira tiriliyan 6.31 wajen biyan basussuka.
Ya bayyana cewa an tsara kasafin bisa kintacen cewa Gwamantin Tarayya za ta samu kuɗin shiga har naira tiriliyan 16.87 cikin 2023. Kuma ana sa ran a riƙa haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 1.69 a kowace rana, yayin da aka yi kintacen cewa za a riƙa sayar da kowace ganga ɗaya kan Dalar Amurka 70.
Wannan kasafin wanda aka raɗa wa suna Kasafin Rage Giɓi Da Rage Ciwo Bashi, ya nuna bai ci sunan sa ba, domin za a ciwo har naira tiriliyan 8.80 a matsayin bashi cikin 2023.
Yayin jawabin sa, Buhari ya yi bitar ayyukan da gwamnatin sa ta gudanar cikin shekaru bakwai da kuma bibiyar yadda aka kashe kuɗaɗen kasafin 2022.
Discussion about this post