Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa bashin da ke kan wuyan Najeriya ya kai naira tiriliyan 42.8.
Ya yi wannan sanarwa ce lokacin da ya ke karanta jawabin Kasafin 2023 a gaban Majalisar Tarayya, a ranar Juma’a.
Buhari ya ce abin da ake bin Najeriya bashi har zuwa watan Disamba, 2022 naira tiriliyan 39.6.
Ya ce kuɗin sun ƙaru ne a cikin shekarar 2022 zuwa naira tiriliyan 42.8 daga watan Janairu zuwa Yuni, wato cikin watanni shida na wannan shekara ta 2022.
Buhari ya ce gwamnatin sa ta biya kuɗaɗen tallafin fetur har naira tiriliyan 1.59 cikin wannan shekarar, tsakanin Janairu zuwa Yuni.
Da ya koma kan Kasafin 2023, Shugaba Buhari ya ce an yi kasafin Naira tiriliyan 20 51, kuma za a ciwo bashin naira tiriliyan 8:8 a 2023.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar Kasafin 2023 na naira tiriliyan 20:51, a gaban Majalisar Tarayya.
Kasafin wanda ya gabatar a ranar Juma’a, shi ne na takwas kuma na ƙarshe a mulkin sa da ya gabatar.
A cikin jawabin sa, Buhari ya bayyana cewa za a samu giɓi na naira tiriliyan 10.78, amma kuma za a cike giɓin da kuɗaɗen bashin da za a ciwo har naira tiriliyan 8.8.
Haka nan kuma ya ce a cikin kasafin, za a kashe naira tiriliyan 6.31 wajen biyan basussuka.
Ya bayyana cewa an tsara kasafin bisa kintacen cewa Gwamantin Tarayya za ta samu kuɗin shiga har naira tiriliyan 16.87 cikin 2023. Kuma ana sa ran a riƙa haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 1.69 a kowace rana, yayin da aka yi kintacen cewa za a riƙa sayar da kowace ganga ɗaya kan Dalar Amurka 70.
Wannan kasafin wanda aka raɗa wa suna Kasafin Rage Giɓi Da Rage Ciwo Bashi, ya nuna bai ci sunan sa ba, domin za a ciwo har naira tiriliyan 8.80 a matsayin bashi cikin 2023.
Yayin jawabin sa, Buhari ya yi bitar ayyukan da gwamnatin sa ta gudanar cikin shekaru bakwai da kuma bibiyar yadda aka kashe kuɗaɗen kasafin 2022.
Discussion about this post