Darajar naira a Kasuwar ‘yan canji ta yi zubewar da ba ta taɓa yi ba, inda a ranar Alhamis sai da ta kai ana sayen dala ɗaya kan naira 781.
Faɗuwar darajar naira ɗin ya zo ne a ranar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi sanarwar cewa zai sauya launin naira 100, 200, 500 da 1000 domin ya yi maganin tsadar kayayyaki da kuma matsalar tsaro da ‘yan damfara masu buga jabun nairori.
A jihohin ƙasar nan dai ana sayar da dala ɗaya naira 775, Mai saye a hannun ‘yan canji kuma zai saya kan naira 781 a Abuja.
Wasu masu hada-hadar canji sun yi kukan cewa ba su samun dala daga bankuna, tilas sai sun tashi sun yi gaganiyar samu a wurare daban-daban.
A ranar Talata kuwa, darajar naira ta yi zubewar da ba ta taɓa yi ba a kasuwar ‘yan canji, naira 760 daidai da dala 1.
Farashin naira ya yi rugurugun da bai taɓa yi ba a baya, inda a ranar Talata da yamma sai da ta kai har Naira 761 a kasuwar ‘yan canji.
PREMIUM TIMES Hausa ta tababar da cewa a ranar Litinin an sayar da dala ɗaya nairs 755, amma washegari Talata kuma sai da ta kai har naira 760 ake saye, a sayar naira 761.
Wani ɗan canji a Zone 4, Abuja cibiyar ‘yan canji ya shaida wa wakilin mu cewa dala ta yi tsada ne a daidai lokacin da ta ke wahalar samu, kuma ake yawan neman ta.
A ranar Talata da safe an riƙa sayar da dala ɗaya Naira 760, amma da yamma ta sauka zuwa naira 758.
“Sai dai kuma ba a sani ba ranar Laraba ko dala zata yi ƙasa, ko kuma ta ƙara tashi.
Dala na ƙara tsada kuma naira na ƙara faɗuwa warwas a lokacin da masu zuba jari ke ƙaranci a Najeriya.
Gwamnatin Buhari ta hau mulki cikin 2015, cike da alƙawarin za ta maida naira ta koma daidai da dala wajen daraja.
Buhari ya hau mulki lokacin da dala ne naira 220.
Yayin da dala take naira 440 a farashin gwamnati a bankuna, ta na ƙaranci sosai, kuma samun ta sai da dalili ko hanya.
Sanarwar da CBN ya yi cewa zai canja launin takardun kuɗin naira ne ya haukata naira har ta faɗi ƙasa warwas.
A cikin sanarwar, CBN ya bayyana dalilin da ya sa zai canja sabbin kuɗi.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shirya ƙaddamar da sabunta takardun naira, a ranar 15 Ga Disamba, 2022.
CBN ya ce zai canja launin takardun kuɗin ne domin ya yi wa kuɗaɗen da ke hannun jama’a talala, sannan kuma ya taka wa tsadar rayuwa burki.
Wani dalilin kuma da CBN ya bayar, shi ne za a canja wa kuɗaɗen launi ne domin a magance babbar matsalar yawaitar kuɗaɗen jabu.
CBN dai ya yi shirin sauya launin takardar Naira 100, Naira 200, Naira 500 da kuma Naira 1000.
Sabbin kuɗaɗen za su fara shiga hannun jama’a a cikin Disamba. Daga nan kuma a cikin Janairu, 31 Ga wata, 2023 za a daina amfani da tsoffin da a yanzu ke hannun jama’a.
Yayin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ke wa manema labarai bayani a ranar Laraba, ya ce CBN ya sha fama da ƙalubale daban-daban, wanda ya zama barazana ga martabar CBN da martabar Najeriya baki ɗaya.
“Matsalolin da ƙalubalen sun haɗa da kimshe maƙudan kuɗaɗe da jama’a ke yi ba tare da ana juya su ba.”
Ya ce an gano cewa kashi 85% na kuɗaɗen da ake jalautawa a hannun jama’a ba su shiga asusun CBN.
“Ya zuwa cikin watan Satumba,2022, alƙaluman ƙididdiga sun tabbatar da cewa naira tiriliyan 2.73 daga cikin naira tiriliyan 3.23 ɗin da ke juyawa a hannun jama’a, ba su cikin rukunin talalar bankunan ‘yan kasuwa, wato duk su na hannun jama’a.
“Sannan kuma hujjoji sun tabbatar da cewa hakan ya na ƙara haifar da tsadar rayuwa da tsadar kaya, lamarin da rabon da a samu hauhawar farashi sosai kamar bana, tun shekaru 17 da su ka wuce.
Ya kara da cewa ana samun yawaitar ruɓaɓɓu da rududdugaggun kuɗaɗe a hannun jama’a. Kan haka ne ya ce ƙarancin takardun kuɗaɗe masu kyau, marasa datti na rage wa CBN kwarjini. Sannan kuma ya na haifar da tangal-tangal ga tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce sauya launin takardun nairori zai rage yadda ake kinkimar maƙudan kuɗaɗe buhu-buhu ana kai wa masu garkuwa domin biyan diyya.
Sai dai kuma tuni jama’a sun shiga damuwa da ruɗani, musamman idan su ka tuna irin bala’in da aka fuskanta, cikin 1984 lokacin mulkin Buhari na soja, lokacin da aka yi canjin kuɗi.
Discussion about this post