A daidai filin wasa na Ranchers Bees da ke Kaduna ya cika fam da dubban magoya bayan jam’iyyar PDP inda Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na kaddamar da kamfen ɗin sa a jihar, a wani bangaren kuma gwamnonin APC ne ke taron yadda za a tsara tafiyar kamfen din ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, wato Bola Tinubu.
Taron gwamnonin ya kai har cikin dare inda suka tattauna game da taron da kungiyoyin Arewa shuka shirya wa duka ƴan takarar shugaban kasa.
Shi ko Peter Obi na LP tare da ɗan rakarar mataimakin sa Datti Baba-Ahmed sun kai ziyara ga babban shehin malami, Ahmed Gumi a gidan sa dake Kaduna.
Waɗannan taruka duk na da nasaba ne da yadda kowacce jam’iyya za ta karkato da ra’ayoyin jama’a su zaɓi ƴan takarar su.
Sai dai kuma ɗan rakarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso,ya bayyana ceqa ba zai halarci zaman wannan taro na ƙungiya ba saboda za a ƙaƙaba wa Arewa ɗan takara na dole ne.
Ya ce tuni dai jam’iyyar sa ta gano haka daga majiya mai tushe kuma dalilin da ya sa ba zai halarci yaron ba kenan.
Ana sa ran gamayyar ƙungiyoyin Arewa za ta gana da ƴan takarar shugaban kasa a Kaduna yau Litinin.
Discussion about this post