Darektan hukumar NDLEA dake jihar Ebonyi Iyke Uche ya ce dakarun hukumar sun kama masu harkallar muggan kwayoyi a jihar 192 daga watan Janairu zuwa Satumbar wannan shekara.
Uche ya ce ” Duka da cewa jihar ba ta da masu safarar kwayoyi da yawa, mashayanta ne suka fi ya.
” Mun kama masu safarar ganyen Wiwi da kuma giyar gargajiya da ke jirkita kwakwalwar mai kwankwaɗa, da ake kira ‘Mkpurummiri’.
Bayan haka Uche ya ce an gano cewa kusan duka manyan laifukan da matasa ke aikatawa a jihar sai sun yi mankasa da kwayoyi tukunna. Hakan ya sa dole suke yi musu bita wayar musu da dai kai illolin da tattare da hambaɗa, kwanƙwaɗa, ko zuƙar wani abu da ke sanya maye.
Discussion about this post