Dimokradiyya guda daya ce a duniya, manufarta guda d’aya ce. Shine yin aiki da doka da kuma samarwa da mutane ‘yancin rayuwa mai inganci. Saidai yadda ake gudanar da ita yana da alaqa da yadda da mutanen da su ke yin siyasar. Gwargwadon rashin ingancin mutane, haka ita ma take kasancewa.
Tsarin dimokradiyya na Amurka ne. Amurkawa sun gudo wajen dimokradiyya ne don su tsira su samu ‘yanci a shekarun baya. Karanta littafin “African Revolutionary” na Malam Aminu Kano. Asali, tsarin ya zo ne don ya bawa kasashe damar gina kansu. Talakawa ne su ke zaɓar mutanen da za su mulkesu da kansu.
Shin a Najeriya, ana yin dimokradiyya ne don gina kasa?
Talakawan Najeriya ma ba su d’auketa haka ba, ballantana wad’anda su ke kashe kud’insu don a za6esu. Duk lokacin da talaka za a bashi kud’i ya za6i mutum, babu ranar da dimokradiyya za ta samar masa da romonta. Dole wanda ya bayar da kud’in aka za6eshi ya nemi riba har da riba (interest) kafin ya yi tunanin wanda ya bawa kud’i su ka za6eshi tunda abun ya zama kasuwanci ba shugabanci ba.
Kada mu yaudari kanmu. Komai a bayyane yake. Abunda ka shuka a rayuwa, shi za ka girba. Idan fa muna son canjin gaske, gaskiya sai mun ajje kwad’ayinmu da aqidar jami’ya a gefe. Babu yadda za a yi mu samu shugabannin arziki idan mun ce dole sai an za6i jami’yarmu ko da d’an takararta bashi da nagarta. Su kuma wad’anda su ke yin siyasar “tsari”, babu ranar da za su samu abunda su ke so saboda sun siyar da ‘yancinsu.
To menene abunda ya dace a za6e mai zuwa?
Duk d’an Najeriya ya koyi darasi tun daga 1999 zuwa yanzu. A cikin ‘yan takarar shugaban kasa babu bako kamar yadda na fad’a a wata hira da na yi. Don duk mutumin da ya yi shekara talatin a duniya, ya san mulkin Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya san mulkin Tinubu a Lagos a matsayin gwamna, ya san na Kwankwaso a Kano a matsayin gwamna, ya kuma san na Peter Obi a Anambra a matsayin gwamna. Abu ne mai sauki a tantance kowa a cikinsu. Saidai idan son zuciya, kwad’ayi ko aqidar jami’ya ne zai hanamu yiwa kanmu adalci.
A wannan lokacin ne za a tabbatar da halin talakan Najeriya. Idan har mu ka bar son zuciya ya cucemu, watarana sai tsakanin ni da ku wani ya gudu daga Najeriya saboda kuncin rayuwa.
Allah ya sa mu ga alheri a zabe mai zuwa.
Discussion about this post