Hukumar NAPTIP reshen jihar Anambra ta kama wata a kauyen Amikwo dake karamar hukumar Awka ta kudu da laifin kashe ‘yar shekara uku da dukan tsiya.
Matar mai suna Chinelo Udogu ta jefar da gawar yarinyar a cikin wani daji bayan ta kashe ta.
Babu wanda ke da masaniyar lokaci ko ranar da Chinelo ta kashe yarinyar domin lokacin da NAPTIP ta gano gawar yarinyar ta fara rubewa.
Bincike ya nuna cewa yarinyar ‘yar uwar Chinelo ne kuma iyayen yarinyar sun bada ‘yar su ga Chinelo amana ta zauna da ita tana taya ta aikace aikace don zumunta amma sai ta kashe ta.
Chinelo ta bayyana wa hukumar cewa ba da niyyar kashe yarinyar ta rufe ta da duka ba abin ya zo da tsautsayi ne. ” Ko da na ke dukan ta da na fahimci ta suma na yi gaggawar kai ta asibiti amma da yake ya zo da ajali sai ta cika.
“Daga asibitin sai na dauko gawar yarinyar na jefar a daji na yi tafiya ta gida.
Daga nan sai hukumar NAPTIP ta tilasta Chinelo ta dauko gawar daga dajin da ta yasar sannan ta mika ta ga ƴan sanda.
Kakakin rundunar Tochukwu Ikenga ya tabbatar da haka yana mai cewa fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka ne za ta ci gaba da bincike.
Discussion about this post