Hukumar kwastam ta shiyar zone A ta kama bindiga kiran ‘pump action’ guda daya, bindigogi biyu na hannu da harsasai 35 daga wurin ƴan sumoga a garin Idiroko a jihar Ogun.
Mukaddashin shugaban hukumar Hussein Ejibunu ya sanar da haka a taron manema labarai da aka yi ranar Laraba a jihar Legas inda yake bayyana aiyukan da hukumar ta yi a watan Satumba.
Ejibunu ya ce ‘yan sumogal ɗin sun arce cikin daji a lokacin da suka hango jami’an kwastam.
Wasu abubuwan da hukumar ta kama a watan Satumba sun hada da buhunan shinkafar waje 7,328, lita 121,550 na man fetur, katan 68 na naman talo-talo, kiret 37 na kwan kaji da aka boye a buhunan shinkafa, kwalaye 250 na ganyen wiwi da kayan sojoji 10.
“Babban kamu da hukumar ta yi shine kama daurin kayan gwanjo guda 1,955 da aka boye a kangon gini a jihar Legas.
Ejibunu ya ce hukumar ta kuma kama jarkunan man fetur da aka boye a cikin buhuna a Badagry.
Ya ce rundunar ta kama mutum biyar da suke da hannu wajen da shigo da waɗannan kayayyaki da gwamnati ta hana shigowa da su.
A lissafe dai adadin yawan kayan da hukumar ta kama a watan Satumba ya kai Naira miliyan 622.4 sannan hukumar ta kama kudi har Naira miliyan 107.8.
Babban kotun gwamnatin tarayua ta yanke was mutum shida hukunci bayan an kama su da laifin shigo da kayan da gwamnati ta hana.
“Idan ba a manta ba gwamnatin Najeriya ta hana shigo da gwanjinan kayan sawa domin kare lafiyar mutane da farfado da masana’antun sarrafa kaya a kasan.
“Gwamnati ta ce kungiyar lafiya ta duniya WHO ta ce saka kayan gwanjo wanda ba a wanke ba na cutar da lafiyar mutum domin ana iya kamuwa da cutar kyasfi, monkey pox da sauran cututtuka.
Discussion about this post