Tsohon Ministan Tsaro Theophilus Ɗanjuma, ya sake gargaɗin ‘yan Najeriya cewa su tashi tsaye su kare kan su daga ‘yan bindiga masu aikata ta’addanci a faɗin sassan ƙasar nan.
Ɗanjuma ya sake yin wannan kira da gargaɗi ne a lokacin da ya ke jawabi yayin bada sandar girma ga sabon Basaraken Wukari, Aku Uka, Manu Ali, a Wukari.
Gwamna Darus Ishaku na Taraba ne ya naɗa Aku Uka cikin 2021, bayan mutuwar sarki Shekarau Angyu, wanda ya shafe shekaru 45 ya na mulki.
Ɗanjuma ya ce gargaɗin da ya fara yi wa ‘yan Najeriya shekarun baya cewa su tashi su kare kan su, ba su ɗauke shi da muhimmanci ba, shi ya sa aka tsinci kai cikin mumnunan halin da ake ciki a yanzu.
“Roƙon da na ke wa sabon Aku Uka shi ne ka rungume mu hannun biyu, ka haɗa kan mu ta yadda za mu iya kare kan mu daga abokansa nan gabar ƙasar nan.
“Cikin 2017 lokacin da na fara yin gargaɗin cewa mu tashi mu kare kan mu, an kafa wani kwamitin wofi ya yi bincike, amma ya ce wai ƙarya na ke yi, babu wata matsalar tsaron da zan iya bayarwa hujja.
“To a yau dai ga hujja nan a faɗin ƙasar nan ko’ina, daga wanda ya ɗanɗana azabar, sai wanda ya yi da kuma wanda ya gani. Kashe-kashen jama’a kawai ake yi ana mamaye masu ƙasa da gonaki a dukkan wurare.
“Ni ba zan ba ku makamai ba, amma ku ma ku gano ta inda ‘yan bindiga ke samun makamai, kuma ku mallaki na ku,” inji Ɗanjuma.
Gwamna Darus Ishaku ya miƙa wa Aku Uka sandar mulki, kuma ya yi kira a gare shi ya haɗa kan al’ummar masarautar sa domin a samu zaman lafiya da yalwa a jihar Taraba.
Ishaku ya jinjina wa Ali dangane da ɗaga likkafar sarautar sa zuwa Babban Sarkin Ƙasar Kwararrafa. Daga nan kuma ya roƙe shi ya yi amfani da ƙwarewar da ya ke da ita wajen wanzar da zaman lafiya da kawo ci gaba a Jihar Taraba.
Shi kuma Sultan na Sokoto Sa’ad Abubakar ya roƙi matasan Wukari su riƙa sauraren Basaraken Wukari ɗin domin a samu gudanar da zaɓen 2023 cikin kwanciyar hankali.
Tun da farko sai da Babban Sakataren Hukumar Ƙananan da Harkokin Sarautun Gargajiya, Bello Yerro ya yi kira ga Aku Uka Ali cewa ya yi aiki tare da sauran sarakunan masarautun jihar Taraba domin jaddada zaman lafiya.
A jawabin sa, Aku Uka kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Taraba, ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai daci gaban jiha da Najeriya baki ɗaya.
Cikin waɗanda su ka halarci bikin miƙa Sandar Mulki ga Aku Uka Ali na Wukari, har da Gwamna Simon Lalong na Filato.
Discussion about this post