Ɗan hada-hadar hodar Ibilis mai suna Emeka Ezenwanne, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja yadda ya bai wa jami’an tsaron filin jirgin sama kuɗi a filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Enugu, domin su ɗaga masa ƙafa ya shigo da koken cikin Najeriya.
Ezenwanne ɗaya ne a cikin mutum biyar da NDLEA ta gurfanar kotu bisa zargin su da shigo da ƙwaya, a shari’ar Abba Kyari, wanda ake tuhuma da safarar muggan ƙwayoyi cikin Najeriya.
Ezenwanne da Chibunna tun cikin watan Yuni ne kotu ta ɗaure kowanen su shekaru biyu a gidan kurkuku, bisa laifin shigo da hodar Ibilis daga Ethiopia.
A ranar Laraba ce Kwamandan NDLEA Mohammed Aja ya shaida wa kotu cewa jami’an su a filin jirgin sama na Enugu sun ƙi kama Umeibe da Ezenwanne lokacin da su ka sauka a filin jirgin, a ranar 19 Ga Janairu.
Ya tabbatar da haka a lokacin da lauyan Kyari mai suna Onyechi Ikpeazu ke yi masa tambayoyi.
NDLEA sun zargi Kyari da wasu jami’an da ya ke aiki da su a lokacin da laifin gurɓata hodar Ibilisin ɗin, bayan sun kwace ta daga hannun masu laifin su biyu.
Da ya ke bayar da shaida ranar Alhamis a kotu, Ezenwanne wanda ke zaman kurkukun ɗaurin shekaru biyu, ya shaida wa kotu cewa ya shiga Ethiopia da
hodar Ibilis ɗin daga Brazil.
Ezenwanne ya ce ya tafi Addis Ababa ranar 15 Ga Janairu domin karɓar muggan ƙwayoyin da aka lodo a cikin jirgin Ethiopian airways daga Brazil.
“Ranar 16 Ga Janairu wajen ƙarfe 8:30 jirgin ya sauka. Nan da nan sai wani mai suna Alhaji ya kira ni.”
Daga nan ya ce sai Umeibe wanda aka ɗaure su tare shi ma aka kira shi ya fara karɓar na sa sunƙin na hodar Ibilis daga wani dillalin muggan ƙwayoyi wanda ɗan aiken wani mai suna Owolabi ne.
“A ranar 19 Ga Janairu da misalin ƙarfe 8 na safe mu ka hau jirgi mai zuwa Enugu daga Addis Ababa. Lokacin da mu ka isa filin jirgin Enugu, na fito daga filin jirgi. Na tsaya wurin ajiye motoci ina jiran fitowar Umeibe.”
Ya ce sun fara cin karo da matsala lokacin da Umeibe ya faɗa hannun wasu jami’an tsaron farin kaya ‘yan sanda, waɗanda daga baya su ka gano cewa ‘yan sandan IRT ne.
“Sun yi cacukui da ni, kuma su ka damƙe Umeibe. Su ka fito da rigunan su na IRT su ka sanya. Daga nan na gane ‘yan sandan IRT ne.”
“A filin jirgin Enugu an nemi na bayar da kuɗi ga jami’an da za su binciki jaka ta. Na ba su Naira 10,000, su ka bar ni na shige salum-alum,” Cewar Ezenwanne a gaban kotu.
Bayan sun bayar da kuɗi ga sun fita jami’an IRT (wato yaran Abba Kyari su ka kama su, bayan an kwarmata masu).
Daga nan aka tattago su zuwa ofishin IRT na Abuja, sannan aka damƙa su ga NDLEA.
Ya ce amma da aka zo ofishin NDLEA na Abuja, sai su ka fahimci daga cikin sunƙin hodar Ibilis 10 ɗin da aka kama a hannun su, babu guda biyu, saura 8. Na cikin jakar aboki na 12 ne.
Lauyan Kyari ya yi masa tambaya, inda ya ce sau biyu kacal ya taɓa shigo da hodar Ibilis cikin Najeriya. Kuma ya tambaye shi ko ya yi ido da ido da Abba Kyari? Ya ce bai taɓa yin ido huɗu da Abba Kyari ba.
Discussion about this post