Ɗan Majalisar Tarayya Denis Idahosa, ya yi kakkausan kira cewa matsawar ana so a rage kashe kuɗaɗen gwamnati barkatai, to sai fa an rushe Majalisar Dattawa kawai.
Idahosa wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisa mai lura Bin Ƙa’idojin Majalisa, ya ce Majalisar Dattawa ba ta da wani amfani, “saboda yawancin aikin majalisa duk a Majalisar Tarayya ake yin su.”
Majalisar Dattawa dai mambobin ta 109, inda uku su ka fito daga kowace jiha, sai FCT Abuja mai Sanata ɗaya ƙwal.
Idahosa ya ce, “na yi amanna cewa in dai ana so a rage kashe kuɗaɗen gwamnati barkatai, to ya zama dole sai an rushe Majalisar Dattawa. Saboda yawancin aikin dai a Majalisar Tarayya ake yin sa.
“A tuna ana biyan mu albashi da alawus-alawus. Amma zaman ranaku uku mu ke yi a sati. To me zai hana a rushe Majalisar Dattawa, sai a ƙara wa Majalisar Tarayya ranakun aiki daga kwanaki uku zuwa kwanaki biyar?”
An daɗe ana ƙorafi dangane da cancanta ko rashin cancantar Majalisar Dattawa a dimokraɗiyyar Najeriya.
Da dama na ganin cewa kamata ya yi kowa ya yi zaman sa a gida kawai. Sai ranar taro a riƙa gayyato su jifa-jifa, amma ba su je Abuja su yi zaman-dirshan ba.
Sannan kuma a duk shekara ana fama da ƙadabolo da Majalisar Dattawa dangane da yadda ta ke cushen ayyukan mazaɓu a cikin kasafin kuɗi, wato ‘budget padding’.
Bincike kuma ya nuna akasarin kuɗaɗen cushen ayyukan mazaɓun, wato ‘constituency projects’, duk karkatar da kuɗaɗen ake yi.
Ayyukan da dama ba a kammala su, wasu ko farawa ba a yi bayan an fitar da kuɗaɗen, wasu kuma ana fitar da kuɗaɗen ayyukan har sau biyu.
Discussion about this post