Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana cewa an fara biyan ta kashi 13% bisa 100 na rarar ribar ɗanyen mai, wanda gwamnatin Tarayya ke bai wa jihohi masu arzikin ɗanyen mai a duk wata.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kogi, Kingsley Fanwo ne ya bayyana haka bayan kammala taron Majalisar Zartaswa na Jihar Kogi, a ranar Alhamis.
Fanwo ya ce Gwamna Yahaya Bello ne ya yi masu wannan albishir a lokacin zaman majalisar a ranar Alhamis.
Sai dai kuma bai bayyana ko naira nawa ne aka fara bai wa jihar ba.
Hukumar Raba Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (RMFAC) ce ta amince da jefa sunan jihar Kogi. Jerin Jihohi masu arzikin ɗanyen mai, bayan gano rijiyar mai daya a cikin 2021.
Gwamnatin Kogi ta shiga sahun jihohi masu arzikin ɗanyen mai.
Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana cewa an fara biyan ta kashi 13% bisa 100 na rarar ribar ɗanyen mai, wanda gwamnatin Tarayya ke bai wa jihohi masu arzikin ɗanyen mai a duk wata.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kogi, Kingsley Fanwo ne ya bayyana haka bayan kammala taron Majalisar Zartaswa na Jihar Kogi, a ranar Alhamis.
Fanwo ya ce Gwamna Yahaya Bello ne ya yi masu wannan albishir a lokacin zaman majalisar a ranar Alhamis.
Sai dai kuma bai bayyana ko naira nawa ne aka fara bai wa jihar ba.
Hukumar Raba Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (RMFAC) ce ta amince da jefa sunan jihar Kogi cikin Jerin Jihohi masu arzikin ɗanyen mai, bayan gano rijiyar mai daya a cikin 2021.
“Ayyukan da wannan gwamnati ta yi a zahiri sun tabbatar da irin gagarimin ci gaban da mu ka kawo a fannoni daban-daban.
“Wannan sabon gagarimin ci gaban fara karɓar kashi 13% na rarar ribar ɗanyen mai, ko shakka babu zai ƙara mana ƙaimin ƙara zage damtsen yi wa jama’a da jiha baki ɗaya aiki tuƙuru.
“Lokacin da Gwamna ya ke mana albishir da fara biyan Kogi kuɗaɗen, ya ce ya na cikin zumuɗi da murnar sanar da mu fara karɓar kuɗaɗen, kuma an saka Kogi a cikin jihohi masu arzikin ɗanyen mai.
Discussion about this post