• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

    Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

    KALUBALEN DA KE GABAN MAJALISAR WAKILAI TA ƘASA: Gaganiya da matsalar raɗaɗin tsadar rayuwa, matsalar tsaro da sauran su da ake fuskanta a kasa

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    RASHIN TSARO: Tinubu ya amince da sayo jiragen sama masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya – Lagbaja

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    Ƴan ta’adda sun gamu da fushin sojojin Najeriya, sojoji sun kashe 50 sun kama 60

    GRAINS MARKET AT KAFIN MADAKI DISTRICT IN GANJUWA

    Yari ya raba tallafin tirela 145 cike maƙil da buhunan masara 145 ga mabuƙata a Zamfara

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

GUMURZUN YAƘIN 2023: Wasu dattawan PDP na so Atiku ya sauya Babban Kwamanda da wasu baraden yaƙi

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
October 13, 2022
in Manyan Labarai
0
2023: Ko ana ha-maza-ha-mata sai PDP ta ci Legas, kuma ta kafa gwamnati a jihar – Atiku

Mako ɗaya da fara kamfen na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na PDP, wasu masu kiran kan su ‘Dattawan PDP Magoya Bayan Atiku’, sun yi tattaki har gidan sa a Abuja, su ka kai masa takardar ƙorafin cewa ya gaggauta sauya Babban Kwamandan Yaƙin neman zaɓe da kuma wasu Baraden Yaƙin kamfen ɗin.

A cikin wasiƙar, sun bayyana cewa akwai buƙatar yi wa Rundunar Yaƙin Shugaban Ƙasa ta Atiku Abubakar (PCC) garambawul, domin a kauce wa sake maimaita babban kuskuren da aka yi a yaƙin neman zaɓen 2019, inda Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, wato Gbenga Daniel ya fice ya koma wata jam’iyyar ana tsakiyar yaƙi.

A kan haka ne dattawan ke roƙon a gaggauta naɗa Raymond Dokpesi ya jagoranci rundunar yaƙin ta Atiku 2023.

Sun bayyana cewa Dokpesi ya fi cancanta, domin ya yi a n gani sosai a 2019, kuma ya nuna tsananin kishin jam’iyya da kishin ɗan takarar ta.

Shugaban ƙungiyar fattawan mai suna Lawrence Okojie ne da Sakatare na Ƙasa Peters su ka sa wa takardar hannu.

Cikin waɗanda su ka yi wa manema,labarai jawabi bayan sun miƙa koken su a gidan Atiku, har da Shugabar Reshen Mata na dattawan, Deborah Makinwa.

Sun ce a cikin Mataimakan Daraktoci akwai waɗanda kishin jam’iyyar da kuma jajircewar su bai kai har cikin zuciyar su ba.

Don haka su ka nemi a ƙyale kowane darakta ya naɗa mataimakin da ya gamsu da aikin sa.

Wannan ƙorafi ya zo ne kwana biyu bayan Sanata Ken Nnamani ya ce ganganci ne ya sa PDP ta fara kamfen ba tare da gwamnonin ta biyar ba.

Tsohon Gwamnan Jihar Enugu, kuma Sanata a yanzu, Ken Nnamani, ya ce babban kuskure ne da ganganci da har jam’iyyar PDP ta fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa, ba tare da gwamnonin jam’iyyar biyar daga kudu ba.

Nnamani ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES a ranar Talata.

Ya ce kwata-kwata ba daidai ba ne, kuma kasada ce babba a ce PDP ta fara yaƙin neman zaɓen ta a kudu, Jihar Akwa Ibom, ba tare da gwamnonin kudu biyar da ke cikin jam’iyyar ba.

Ya ce bai ga yadda za a yi nasara ba, idan gwamnonin biyar su ka ƙi bayar da haɗin kai lokacin zaɓe a jihohin su.

Ya ce ko an ƙi, ko an so gwamnonin jagorori ne a jihar su, kuma su ne kusa da jama’ar karkara ba ‘yan siyasar Abuja ba.

“Shi ɗan siyasar Abuja aikin shi kaɗai ya baza babbar riga ya shirya taron gangami, daga ranar kuma ba a ƙara ganin shi a jihar. Gwamna shi ne mai jama’a. Don haka idan ka wulaƙanta gwamna, to tamkar ka haɗa ne har da na ƙarƙashin sa duk ka wulaƙanta su.”

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Jirgin yaƙin PDP na tangal-talgal, saboda gwamnoni biyar sun ƙi hawa a yi lodin kamfen tare da su.

Duk da cewa jam’iyyar PDP ta ƙaddamar da kamfen ɗin yaƙin neman zaɓen 2023 a Akwa Ibom cikin nasarar tara ɗimbin jama’a, ƙaurace wa gangamin da gwamnoni biyar su ka yi ya nuna har yanzu akwai jan-aiki ga Atiku sosai kafin ya dangana da kujerar shugaban ƙasa.

Gwamnonin guda biyar da ba su halarci taron ba, sun haɗa da Nyesom Wike na Jihar Ribas, Seye Makinde na Jihar Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Ikpeazu Okozie na Abiya sai kuma Samuel Ortom na Jihar Benuwai.

Su huɗun su na goyon bayan Wike ne, wanda ya jagorance su bijire wa PDP bayan an tsayar da Atiku takarar shugaban ƙasa.

Su biyar ɗin dai su na neman tilas sai shugaban PDP, Iyorchia Ayu ya sauka a naɗa ɗan Kudu, domin a tabbatar da adalci a shugabancin PDP.

Gangamin wanda PDP ta yi a Filin Wasa na Godswill Akpabio International Stadium, ya cika fal da magoya bayan PDP, inda a wurin Atiku ya sha alwashin cewa idan aka zaɓe shi, to za a yi bankwana da talauci da matsalar tsaro da rashin aikin yi a Najeriya.

Idan ba a manta ba, waɗannan gwamnoni biyar ba su halarci taron ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na PDP ba.

Masu bibiyar lamarin siyasa na ganin cewa PDP za ta iya fuskantar matsala matsawar ba ta sasanta da gwamnonin biyar ba.

Su Wike dai su na jin haushin yadda ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma Shugaban PDP Iyorchia Ayu duk su ka fito daga yankin Arewa.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da rundunar yaƙin Bola Tinubu na APC ta ce, rikicin da hasalallun gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne ga APC.

Rundunar Yaƙin Tinubu 2023 ta ce turnuƙun rikicin da wasu hasalallun gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne ga jam’iyyar APC.

CIkin wata sanarwa da ɗaya daga cikin Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Tinubu, Festus Keyamo ya fitar a ranar Asabar, ya ce rikicin da ke faruwa a cikin PDP ya nuna cewa jam’iyyar ba za ta iya riƙe mulkin Najeriya ba, tunda har yau ta kasa ma sasanta rikicin da ke cikin gidan ta.

Keyamo ya ce PDP ba za ta iya haɗa kan Najeriya ba, tunda ta kasa haɗa kan iyayen jam’iyyar PDP ɗin.

Hasalallun gwamnonin dai bisa jagorancin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, har yau sun ƙi goyon bayan takarar shugabancin ƙasa da Atiku Abubakar ke yi, bisa dalilin cewa babu adalci wajen raba muƙaman jam”iyyar, saboda an damƙa shugabancin PDP ga ‘yan Arewa, inda kuma a yankin ne ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya fito.

Gwamnonin dai sun gindaya cewa kafin su fara goyon bayan Atiku, tilas sai Shugaban PDP, Iyorchia Ayu ya sauka an naɗa ɗan Kudu, domin a yi adalci.

Sannan kuma zargin da Wike ya yi wa Ayu kwanan nan, cewa ya raba wa shugabannin jam’iyyar cin hanci, kuma ya karɓi naira biliyan 1 a hannun wani a Legas, ya ƙara jefa PDP cikin ruɗani.

Keyamo ya ce har yau jam”iyyar PDP ba ta tuba daga ɗabi’ar ta na wawurar kuɗaɗe ba. Don haka ba za ta yaudari ‘yan Najeriya ba a zaɓen 2023.

“Ai mu rikicin da wasu gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne a gare mu. Sun kasa haɗa kan su, kuma rikicin wuru-wurun kuɗaɗe ya ƙara dagula PDP. Hakan ya nuna har yau ba su tuba daga ɗabi’ar su ta sata ba.

Keyamo ya ƙara caccakar PDP cewa sun bi son ran Atiku, sun ƙi bai wa Kudu takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, kamar yadda su ka yi yarjejeniya a baya.

Tags: AbujaAtikuKadunaLabaraiNewsPDPPREMIUM TIMES
Previous Post

Sanatoci sun wargaje injin Kasafin 2023, sun ce akwai ƙura, hazo da dattin ruwan kwatami a ciki

Next Post

” Na ba ka awa 48 ka rufe kamfanin simintin ka na Obajana, ko mu hukunta ka – Yahaya Bello ga Aliko Ɗangote

Ashafa Murnai

" Na ba ka awa 48 ka rufe kamfanin simintin ka na Obajana, ko mu hukunta ka - Yahaya Bello ga Aliko Ɗangote

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda gaggan ‘Yan bindiga da suka addabi Arewa su ka yi taron sulhu da tawagar gwamnatin Tarayya a Katsina
  • An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru
  • TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa
  • FCT ABUJA: Wike ya kori shugabanni da daraktocin hukumomi 21
  • Kotu ta yi watsi da ƙarar PDP a Shari’ar gwamnan Kaduna, dalili kuwa shine wai ba ta shigar da ƙara da wuri ba

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.