Ganduje ya ce gwamnati ta yi haka ne domin rage raɗaɗin wahalar balaguron neman motar hawa da kanawa ke yi a jihar.
Da yake jawabi a wurin ƙaddamar da motocin, gwamna Abdullahi Ganduje ya ce gwamnati ta yi wannan huɓɓasa ne domin rage raɗaɗin wahalar zirga-zirga da mutanen jihar ke fama da shi.
” Musamman mutanen yankin Jogana, Yankura zuwa Janguza, duk waɗanan motoci za su rage musu wahalar zirga-zirga.
A cewar Ganduje an samar da manyan motoci 100 sannan da ƙananan motoci 50. Kuma ya ce an saka karin manyan motoci 200 a cikin kasafin kuɗin jihar ta 2023.
Gwamna Ganduje ya ce ginae ginen da aka yi na faɗada hanyoyi da dama, gadar sama da na kasa da sauran ababen more rayuwa da dama da ake ganin sun zama wajibi don samun ci gaban kasuwanci da kuma samar da ayyukan yi.
“Ya zuwa yanzu, rashin samun ingantacciyar hanyar zirga-zirgar jama’a ya haifar da yawaitar Kekuna a matsayin babbar hanyar jigilar jama’a a cikin babban birnin Kano.
“Sakamakon haka, cunkoson ababen hawa ya kai wani matsayi da ke bukatar lalli dole gwamnati ta dauki irin wannan mataki domin kawo karshen wannan matsala.
Daga nan sai gwamna Handuje ya ce ” An sayo motocin bas da tasi akan Naira biliyan 2.5.
Discussion about this post