A cikin makon da ya gabata an yi ta cin karo da kanun labarai dangane da rikicin da ya dabaibaye PDP iri daban-daban. Yau ka ji an ce PDP “kaza-kaza”, gobe ma haka.
To amma ba fa PDP ce kaɗai ke fama da rikici ba. Jam’iyya mai mulki ita ma ruwan rikici ya cinye ta iyar wuya, kamar yadda ruwan ya yi ambaliya cikin gidan PDP.
APC na fama da rigimar rashin amincewa da titikin Muslim-Muslim da wasu ‘yan jam’iyyar su ka ƙi yi.
Akwai kuma sabon rikicin da ya ɓallo ruwa sanadiyyar kafa rundunar yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu. Sai kuma yanaɗiɗin da ake yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu cewa ba shi da kumari, kuzari, ƙarfin jiki da ƙoshin lafiyar da zai iya takarar shugabancin ƙasa da kuma iya mulkin ma ɗungurugum.
Sai da kuma jama’a da dama sun fi maida hankali kan rikicin PDP, wanda ake ganin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, kuma ya na ci gaba da faɗaɗa, tare da yi wa jam’iyyar illa.
Matsalar Ayu A Shugabancin PDP:
Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu dai ba shi ya zaɓi kan sa ba, zaɓar sa aka yi bisa ƙa’ida. Don haka ba daidai ba ne a riƙa alaƙanta shi da matsalar PDP.
Sai dai kuma idan aka yi la’akari da cewa hawan sa shugabancin jam’iyyar ya haifar da zaizayewar ta, wannan ma abin dubawa ne.
Na farko dai a ƙarƙashin shugabancin Ayu aka samu saɓani da Rabi’u Kwankwaso, ya fita daga PDP, ya shiga NNPP, kuma ya raya jam’iyyar har a Arewa ana yi mata kallon ita ce ta uku wajen ƙarfi.
A ƙarƙashin shugabancin Ayu Peter Obi ya fice daga PDP, ya koma LP, kuma ya fito takarar shugabancin ƙasa. A Kudu ana ganin LP ce ta uku wajen ƙarfi.
Ashe kenan da PDP ba ta rabu da Peter Obi da Kwankwaso ba, da ƙarfin da ta ke da shi a yanzu ya nunka kenan. Hakan zai iya bai wa jam’iyyar damar lashe zaɓen 2023 fitinkau. To sai dai rikicin cikin gida ya sa ta rabu da waɗannan, kuma ta ci gaba da afkawa cikin wasu rikice-rikicen.
Kaka-gidan Tsoffin ‘Yan Alewa A PDP:
Jam’iyyar PDP ta sha kaye a zaɓen 2015 sanadiyyar baƙin jinin da APC ta riƙa goga mata a yayin kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa.
An riƙa aibata jiga-jigan PDP daga sama har ƙasa, Majalisar Tarayya, Majalisar Dattawa, Gwamnoni, Ministoci da Shugaban Ƙasa a wancan lokacin duk an saɓule masu riguna a wajen kamfen ɗin APC.
Sai dai kuma yayin da wasun su su ka koma APC su ka narke cikin mulkin Buhari, sauran jiga-jigan jam’iyyar na ciki ba su je ko’ina ba. Kuma su ne dai ke ci gaba da jan ragamar ta a yanzu kama daga shugabancin jam’iyya zuwa takarar shugaban ƙasa, duk tsoffin ‘yan PDP ɗin ne.
To abin lura a nan shi ne, duk da talakawa sun ji jiki, kuma su na ci gaba da rayuwar ƙunci sanadiyyar tsadar rayuwa da matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan, to kuma har yanzu talakawa ba su gama karɓar PDP hannu bibbiyu ba.
Rashin ganin matasa sosai a sahun gaban tarukan jam’iyya da manyan muƙamai na rage wa PDP karsashi.
To sai dai kuma alamomi na nuni da cewa a jihohi da dama a Arewa PDP za ta kwashi ƙuri’u da dama, musamman daga ɓangaren magoya bayan APC waɗanda ake ganin cewa za su yi ‘taƙiyya’ a lokacin zaɓe, saboda wasu dalilai na jin jikin halin ƙuncin rayuwa a hannun ‘yan bindiga da su ka yi kaka-gida a Arewa.
Jajircewar Atiku Da Daburcewar Sa A Rikicin PDP:
A ƙarƙashin batutuwan rikicin PDP, ɗimbin masu sharhi na ganin cewa babu wani dalilin da zai sa Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya haƙiƙice sai Iyorchia Ayu ya sauka daga shugabancin PDP. Su na ganin Ayu ba shi ne matsala ba. A ganin su, Atiku ne ya janyo matsalar, domin ya karya batun yarjejeniyar cewa jam’iyyar za ta bar wa ɗan kudu takarar shugaban ƙasa. Kuma dalili kenan kudu ta bar wa Arewa shugabancin PDP, har aka zaɓi Ayu ɗan Arewa ya zama shugaban jam’iyya.
Atiku dai ya ce ba shi da ikon cire Ayu, idan ba shi ne ya sauka don raɗin kan sa ba.
Garin Gyaran Doro An Karya Ƙugu: Zargin Watandar Cuwa-cuwar Kuɗaɗe:
Yayin da ake ta ƙoƙarin ganin an ɗinke ɓarakar rigar PDP, can a sama kuma sai lamari ya ƙara lalacewa, inda aka zargi Iyorchia Ayu ya raba wa wasu jiga-jigan PDP miliyoyin kuɗaɗe don su ci gaba da goyon bayan sa.
An raba masu daga mai naira miliyan 28.8 zuwa mai naira miliyan 36. Sai dai kuma waɗanda aka raba wa kuɗaɗen wai da sunan kuɗaɗen kama gidan haya, sun mayar wa PDP kuɗaɗen bayan sun ga yadda aka riƙa yamaɗiɗi da sunayen su a jaridu da shafukan sadarwa na soshiyal midiya.
Fallasa sunayen waɗanda aka raba wa kuɗaɗen ya fito ne sati ɗaya bayan Wike ya yi zargin cewa Ayu ya raba cin hancin naira biliyan ɗaya don a goyi bayan kafa ya sauka daga shugabancin jam’iyya.
A yanzu da aka buga kugen fara yaƙin neman zaɓe, masu lura da al’amurran siyasa sun zuba ido su ga yadda zaratan rundunar yaƙin PDP su 600 za su fafata da sauran jam’iyyu.
Sai dai kuma matsawar ba a warware kwamacalar rikicin Wike ba, to akwai sauran aiki a gaban PDP, musamman ma ganin cewa a Arewa ba a san mataimakin takarar shugaban ƙasa na Atiku ba, wato Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta.
Da dama na ganin cewa kamata ya yi tun da farko Atiku ya ɗauki Wike a wuce wurin. A ganin su, ai Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce, ‘ka riƙe mahaukacin ka, don ya yi maka maganin mahaukacin wani.’
Discussion about this post