Hukumar Tsaro na DSS ta ja hankalin mazauna Babban Birnin Tarayya Abuja cewa kowa ya ci gaba da gudanar da harkokin sa, kuma ya natsu.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na SSS Peter Afunanya ya fitar, ya ce rundunar SSS na aiki tare da sauran ɓangarorin jami’an tsaro wajen ganin harkoki da rayuwar mazauna Abuja su na tafiya ba tare da tangarɗa ba.
Hakan ya biyo bayan wani gargaɗi ne da Ofishin Jakadancin Amurka da na Birtaniya da ke Abuja su ka fitar a ƙarshen mako, inda su ka gargaɗi ‘yan ƙasar su cewa su ƙaurace wa Abuja, domin akwai ƙishin-ƙishin cewa ‘yan ta’adda na shirin kai hari a birnin.
“Afunanya ya ce ofishin sa na shan tambayoyi dangane da gargaɗin da ofishin jakadancin Amurka ya yi na a daina shiga Abuja.”
Ya ce ita ma Hukumar SSS ta yi wannan gargaɗin cewa akwai yiwuwar neman tayar da fitina a Abuja. Amma kuma Hukumomin tsaro na bakin ƙoƙarin su.
“Yayin da SSS ke kira ga ɗaukacin jama’a su kwantar da hankalin su, hukumar na ƙara yin kira da cewa duk wanda ya ga wanin abin da ka iya zama barazana, to ya gaggauta sanar da jami’an tsaro.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ofisoshin jakadun Birtaniya da Amurka sun gargaɗin ‘yan ƙasashen su cewa su gaggauta ƙaurace wa Abuja.
Discussion about this post