Farashin naira ya yi rugurugun da bai taɓa yi ba a baya, inda a ranar Talata da yamma sai da ta kai har Naira 761 a kasuwar ‘yan canji.
PREMIUM TIMES Hausa ta tababar da cewa a ranar Litinin an sayar da dala ɗaya nairs 755, amma washegari Talata kuma sai da ta kai har naira 760 ake saye, a sayar naira 761.
Wani ɗan canji a Zone 4, Abuja cibiyar ‘yan canji ya shaida wa wakilin mu cewa dala ta yi tsada ne a daidai lokacin da ta ke wahalar samu, kuma ake yawan neman ta.
A ranar Talata da safe an riƙa sayar da dala ɗaya Naira 760, amma da yamma ta sauka zuwa naira 758.
“Sai dai kuma ba a sani ba ranar Laraba ko dala zata yi ƙasa, ko kuma ta ƙara tashi.
Dala na ƙara tsada kuma naira na ƙara faɗuwa warwas a lokacin da masu zuba jari ke ƙaranci a Najeriya.
Gwamnatin Buhari ta hau mulki cikin 2015, cike da alƙawarin za ta maida naira ta koma daidai da dala wajen daraja.
Buhari ya hau mulki lokacin da dala ne naira 220.
Discussion about this post