Gamayyar kamfanonin BUA na Abdulsamad Rabi’u, ya yi watsi da cinikin filin da ya ƙulla da Jihar Kogi, mai faɗin hekta 50,000.
BUA ya ce filin ba shi da wata daraja ko albarkar da za a iya kafa masana’anta a cikin sa.
Tun shekaru 10 da su ka gabata ne dai Gwamnatin Kogi ta gayyaci BUA domin ya sayi filin, amma a yanzu ya ce filin bai cancanci a kafa masana’anta a cikin sa ba.
Cikin wata wasiƙar da BUA ya aika wa Gwamnatin Jihar Kogi, wadda kuma PREMIUM TIMES ta ga wasiƙar, ya ce BUA bai karɓi haƙƙin mallakar filin ba, saboda daga baya an gano kashi 30 bisa 100 a faɗin ƙasar ne za a iya cin moriya kaɗai.
Kamfanin BUA dai ya shahara wajen sarrafa siminti, abincin masarufi, harkar jiragen ruwa, ƙarafa da sauran su.
Rikici ya ɓarke dangane da filin tsakanin BUA da Gwamnatin Kogi cikin wannan wata, inda har Majalisar Jihar Kogi ta nemi kamfanin BUA ya bayyana gaban ta.
Majalisa ta ce tun da aka sayi filin ba a biya ko sisi ba, tun bayan ciniki a shekarar 2012.
Mataimakin Kakakin Majalisar Kogi Alfah Momoh-Rabiu ya ce “ba a biya ko sisi ba.”
Irin haka ne shi ma kamfanin Ɗangote Cement ke fuskantar matsin lamba daga Gwamnatin Jihar Kogi dangane da rikici kan cinikin Obajana Cement PLC, wanda Ɗangote ta saya ya narka shi a cikin Ɗangote Cement.
BUA ya ce cikin yarjejeniyar da su ka yi da Gwamnatin Kogi lokacin cinikin hekta 50,000, gwamanti za ta yi titi a hanyar domin samun sauƙin aiki. Amma har yau ba ta yi komai ba.
“Sannan kuma akwai matsalar tsaro a yankin, ta yi munin da ba za a iya gina masana’anta a yankin ba.”
Discussion about this post