Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa zai gana da gwamnonin Najeriya, domin su amince a saki aƙalla fursunoni 22,680 daga cikin 75,635 da ke tsare a gidajen kurkukun Najeriya daban-daban.
Da ya ke amsa tambayoyin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Aregbesola ya ce ganawa da gwamnonin idan ana so a saki ɗaurarrun ta zama dole, saboda kashi 90 bisa 100 na waɗanda ke tsare a kurkuku duk dokokin jihohi su ka karya, ba dokokin gwamnatin tarayya ba.
Haka nan kuma Aregbesola ya ce kashi 70 cikin 100 na mutum 75,635 da ke tsare a kurkuku daban-daban na Najeriya, duk masu jiran a yanke masu hukunci ne.
Ministan ya ce waɗanda su ka karyar dokar tarayya kuma su na tsare a kurkuku ba su ma kai kashi 10 na mutum 75,635 ɗin da ke tsare a kurkuku ba.
Daga nan ya ce ya zama wajibi a rage yawan waɗanda ke ɗaure a gidajen kurkukun Najeriya 253, saboda da yawan su babu wani dalilin ci gaba da tsare su ake yi.
“Idan masu ruwa da tsaki ba su tashi tsaye sun yi gyara a tsarin shari’a da dokokin hukunta masu laifi ba, to za mu ci gaba da fuskantar cinkoso a gidajen kurkuku ne kawai.”
Ya ce da yawan waɗanda ke tsare su na jiran a yanke masu hukunci, shekarun da su ka daɗe tsare sun wuce na adadin yawan hukuncin ɗaurin da za a yi masu.
“Za ka ga ɗan sane wanda hukuncin sa bai wuce ɗaurin watanni shida ba, amma ya shafe shekaru uku tsare a kurkuku, ya na jiran a yanke masa hukunci.” Inji Aregbesola.
“Ko kuma a kama yaro a ƙarƙashin gada, ba a same shi da laifin komai ba, an tsare shi shekaru a gidan kurkuku. Ka ga lamarin akwai buƙatar gyara kenan.
A kan haka ne Minista Aregbesola ya ce ya rubuta wa Kungiyar Gwamnonin Najeriya wasiƙar neman zama su tattauna lamarin.
Nan Da Watan Disamba Za A Kakkaɓe Duk Wata Matsalar Tsaro Baki Ɗaya -Aregbesola:
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan da watan Disamba za a kakkaɓe duk wata matsalar tsaron da ta dabaibaye Najeriya.
Aregbesola ya bada wannan tabbacin lokacin da ya ke tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a Abuja.
Minista ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya bada wa’adin cewa lallai daga nan zuwa Disamba dukkan hukumomin tsaron su tabbatar da sun samar da dawwamammen zaman lafiya a dukkan faɗin ƙasar nan.
Ya ce Buhari ya ce ba zai sauka daga mulki ba tare da ya daƙile matsalar tsaron da ke neman durkusar da ƙasar nan ba.
“Shugaba Buhari ya bada wa’adin nan da watan Disamba cewa Hukumomin tsaro su kakkaɓe duk wata barazanar tsaron da ke addabar rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya nan zuwa watan Disamba.
“Na yi amanna cewa dukkan ɓangarorin tsaron ƙasar nan sun tashi tsaye haiƙan, babu sauran hutu, domin su tabbatar cewa sun kawar da duk wata barazanar tsaro a ƙasar nan.
“Mun maida hankali sosai, da farko misali, sai mu fara tambayar kan mu tukunna, farkon abin da ya wajaba na haƙƙin da ya rataya a wuyan gwamnati, ai shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Saboda haka daga nan zuwa watan Disamba za mu kakkaɓe duk wata matsalar tsaron da ke addabar ƙasar nan.
“Idan ka dubi halin da ake ciki yanzu a Najeriya, zan iya cewa an samu gagarimin ci gaba a cikin ‘yan shekarun nan,” inji Aregbesola.
Aregbesola ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa kafin 2015 babu inda bama-bamai ba su tashi a Najeriya.
Yanzu kuma a ta bakin sa, ya yi babu sauran inda ‘yan Najeriya ke kwana cikin fargaba da tsoron za a dasa masu nakiya a ƙasar nan.
Aregbesola ya danganta fantsamar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan bisa dalilin fatattakar ‘yan ta’adda daga Arewa maso Gabas.
“Kuma mun daƙile masu ɗaukar makamai Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, Kudu maso Yamma kuma mun daƙile ‘yan ƙungiyar asiri.
“Saboda haka nan da ƙarshen shekara ‘yan Najeriya za su yi bankwana da matsalar tsaro,” Inji Minista Aregbesola.
Discussion about this post