Fitaccen malamin Kaduna Sheikh Ahmad Gumi, ya soki kudiriy canja fasalin naira da babban bankin Najeriya ya bijiro da shi a kasar nan
Cikin karatu da yayi a garin Kaduna, Gumi ya ce ana so a canja fasalin kudin Najeriya a wannan lokaci ne don a yi ragaraga da talakawan Arewa.
” A ganina lokacin da aka tsara za ayi wannan canjin kuɗi bai ya daidai ba. Ina takaka zai saka kan sa, an ce wai sai mutum yana da asusun ajiya a banki. Tsakani da Allah mutanen mu dake karkara yaya za su yi da ƴan kuɗaɗen su da suka wahala.
” Eh lallai abi ne mai kyau amma kuma lokacin da aka ɗiba masa ya yi kaɗan matuka. Ya kamata a ce idan aka canja za a samu wani tsawon lokaci mutane suna canja kuɗaɗen su a hankali.
Gumi ya kara da cewa amma salon canjin da gwanatin tarayya ta bijiro da shi bai da ce ba kwatakwata kuma zai talauta mutane ne sannan kuma da saka kasa cikin halin ƙaƙanikayi.
” Kasashen duniya na canja kuɗaɗen su, amma kuma wasu ma ba za ka sani ba sai dai kawai idan ka gani, haka za a yi ta musanya su da tsoffin kuɗi har su daina zagayawa.
” Amma a ce za a bijiro da abu irin haka sannan cikin gaggawa sannan ace wai kuma an kyayyade wani lokaci da dole kowa ya canja kuɗaɗen sa bai dace ba kwatakwata.
A game da dakile kuɗaɗen dake hannun ƴan bindiga, da yiwuwar rasa su, Gumi ya ce ” Idan ma saboda ƴan bindiga ne aka yi haka, toh ai ba sauki za a samu ba, saboda za su iya tilasta mutane su biya kuɗin fansa da kuɗaɗen kasashen waje kamar dala da dai sauransu.
Gumi yayi kira da a sake duba ta wata mahangar yadda zai amfani talaka ba ya daɗa tsananta
Discussion about this post