Ban ma san daga inda zan fara cewa wani abu ba, dangane da yunƙurin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ke yi domin ganin ya sauya fasalin takardun Naira da ya ce za a yi ba. Na tabbatar daga cikin dalilan sa, akwai tsari na ƙwarai. To amma kuma yanayin yadda aka bijiro da batun sauyin kuɗin ne ‘yan Najeriya ba za su yarda da batun ba.
Yayin da kowa har da malamai ke faɗin albarkacin bakin su, ana yin tir da batun sauya launin kuɗin, Ni ma dai ina da ta-cewa, kuma zan ce abin da na ke so na ce cikin wannan ce-ce-ku-ce.
Wane Ne Godwin Emefiele?:
Amma daga farko, bari na fara da tambayar masu karatu: Shin wane ne Godwin Emefiele?
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya zama Gwamnan CBN bayan da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya cire Sanusi Lamiɗo Sanusi. Emefiele na daga cikin waɗanda Shugaba Muhammadu Buhari bai cire daga muƙaman su ba a lokacin da ya zama shugaban ƙasa a 2015.
Emefiele ya na Gwamnan CBN ne aka riƙa jida kuɗaɗen Najeriya, musamman shekara ɗaya kafin ƙarshen mulkin PDP.
Buhari ya hau mulki ya samu dala ɗaya ba ta kai Naira 250. A Najeriya dai Emefiele ne ke riƙe da ragamar Naira da ta Dala. A yau maimakon a ce Naira ta koma daidai da Dala kamar yadda aka yi alkawari, to Dala ta yi tashin da ta kai Naira 781.
Matsayin Emefiele Da CBN A Gwamatance:
Godwin Emefiele da CBN duk su na ƙarƙashin Ofishin Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ne. Duk da cewa zai iya tunkarar Shugaban Ƙasa kai-tsaye domin neman amincewar sa, amma dai ko shakka babu uwa ba ta za yi sa ‘yar ta aure ga mahaifin ta a gidan ko goron gayyata ba a ba shi ba.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe ita ce Minista mafi ƙarfi a Najeriya. Ita ce injin ɗin tattalin arziki. Ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe duk a hannun ta su ke. Ashe kenan ganganci, azarɓaɓi da giribtu ne a ce Emefiele ya yi maganar musanya kuɗaɗe ba tare da tuntuɓar Minista Zainab Ahmed ba.
Baya ga CBN da ke ƙarƙashin ta, akwai irin su Hukumar Tara Kuɗaɗen Shigar Cikin Gida (FIRS), IST, NDIC, Hukumar Kwastan ta Ƙasa, SEC da sauran su.
Bayan haka, duk wanda ya san irin bala’in da masu ajiye da kuɗaɗe su ka sha a lokacin canjin kuɗi cikin 1984, a zamanin mulkin soja na Buhari, to ba zai yi fatan ya na raye ya sake ganin yadda mutane musamman masu kuɗin ƙauye su ka riƙa ɗibga asara, saboda sun kasa cika wa’adin kai kuɗin su a banki. Dubban jama’a a Arewa ƙone na su kuɗaɗen su ka yi, saboda sun zama ciyawa, ba mai karɓa.
Duk wani haske ko alherin da ke tattare da batun sauya fasalin Naira, lamarin ba zai samu karɓuwa daga jama’a ba, saboda akwai wani abu lulluɓe su ke cewa.
Ya kamata Godwin Emefiele ya ɗauki darasi daga Sanusi Lamiɗo Sanusi, wanda duk da gaskiya ce ya faɗa, a ƙarshe sai da aka cire shi daga CBN.
Ya kamata Emefiele ya ɗauki darasi a rigimar Yusuf Usman tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiyar Ma’aikatan Gwmnatin Tarayya (NHIS), a faɗan sa da Ministan Lafiya na lokacin, Adebowale.
Ya kamata Emefiele ya ɗauki darasi daga rigimar tsohuwar Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), Hadiza Bala Usman da Ministan Sufuri na lokacin, Rotimi Amaechi.
Ya kamata Emefiele ya sani cewa ‘yan Najeriya tuni su ka dawo daga rakiyar irin riƙon sakainar kashin da ya ke yi wa naira. Ya hau riƙon CBN ba ta kai naira 200 ba. Amma yanzu a kan idon sa dala 1 ta kai naira 781. Idan har bai Buhari bai maida hankali ya tsige shi ba, to shi ya kamata ya ji kunya ya sauka daga shugabancin riƙon akalar naira da ya ke yi.
Ta yaya ka na kiwon shanu, ga shanun ka sun afka cikin gonakin mu su na ɓarna, sai ka tsaya ka na busa sarewa, har ka na tunanin mu riƙa cewa ‘lallai ka iya busa?’ Shin idan kai ba mai ankarewa ba ne, ai mu kuma ba mahaukata ba ne.
Discussion about this post