Cikin 2020, OCCRP ta fallasa cewa wani binciken bin-diddigin kuɗaɗe da Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi, ya samu Hima d hannu dumu-dumu cikin harƙallar kwangilar safarar muggan makamai ta dala miliyan 240.
Kwafen kwangilar wanda OCCRP ta gani ƙuru-ƙuru, ya nuna Abubakar Hima, wanda ya tashi da kwangilar dala miliyan 240 ba cas ba as, a Nijar, wataƙila kuma wata gadar-zaren ce ya ke ƙullawa.
Farkon wannan isar-ƙadagi dai a Gwamnatin dai gwamnatin Senegal ce ta rattaba hannun kwangila ta shigo da manyan makamai da su kai har na dala miliyan 77. Za a shigar mata da makamai da su ka haɗa da bindigogi samfurin fistol, albarusai da sauran dangogin makamai.
Jama’a dai na yi wa kallon wannan kwangila kallon wani abu ne bambarakwai da ba a saba yin irin ta, kamar ta ko madadin ta ba.
Asarƙalar farko a tashin farko cikin wannan gagarimar kwangila, ita Ma’aikatar Raya Muhalli ce ta shigo da makaman, ba hukumomin soja ba.
Abu na biyu shi ne a lulluɓe cikin duhu aka bayar a kwangilar, a asirce, ba a buga ta a jarida an buga tandar neman kamfanin da ya fi cancanta a ba shi kwangilar ba, kamar yadda ya kamata a yi a ƙa’idance. Amma sai aka bayar a asirce, aka sa mata hannu a asirce, saboda an san an kauce wa tsarin dokokin tsaron ƙasar Senegal.
Ita kuwa kaza mai tone-tone, wato OCCRP, tare da jaridar Haaretz ta Isra’ila, sun ji labarin harƙallar kwangilar, kuma sun samu kwafen takardun bayar da kwangilar. Ai kuwa sai su ka fallasa.
Waɗanda su ka shigo da makaman, wato Lavie Commercial Brokers dai an gano kamfani ne da tantagarya kuma gogarman harkokin komai da ruwan ka, wanda ya shahara a Afrika ta Yamma, Abubakar Hima ya kafa shi.
A baya ana zargin Hima da harƙallar karkatar da miliyoyin daloli daga kuɗaɗen da aka danƙara cikin kwangilar da ake biyan kuɗaɗen da su ka wuce tunanin mai hankali a cikin kwangilar shigo da makamai cikin Najeriya da kuma ƙasar sa, wato Jamhuriyar Nijar.
Wani ƙwararren masani da ya tattauna harƙallar kwangilar Hima a Senegal, ya shaida wa jaridar OCCRP cewa hujjojin da ke nuna cewa ba bisa ƙa’ida aka bai wa Hima kwangilar shigo da makamai a Senegal ba, ita ce kai da gani ka san an nunnunka adadin da ya kamata a ce su ne kuɗin kwangilar na gaskiya.
An fi kiran Hima da sunan sa na ‘yan gayu, kuma ɗan ca-buros, wato “Petit Boube,” Hima gugar ƙarfe ce sha kwaramniya jikin bangon rijiya. Ba sabon-yanka-rake ba ne wajen shiga cikin harƙalla. Ƙasashen Amurka da Afrika ta Kudu sun taɓa ƙwace miliyoyin dalolin harƙallar makamai daga hannun sa.
A Najeriya kuma ana neman sa wurjanjan, saboda zargin aikata laifin harƙallar shigo da makamai, inda ya yi asarƙalar zamba-cikin-aminci a cikin wata kwangilar da shigo da makamai ɗin da gwamnati ta ba shi a cikin 2020.
Jaridar OCCRP dai ta fallasa yadda Hima ke da hannu wajen shirya harƙallar zambar kuɗaɗe har dala miliyan 240 a wani binciken kuɗaɗe da bin-diddigin da Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi.
Da ya ke Hima mutum ne mai wayau da dabara, saboda ya san kurar sa ta yi kuka, an san shi ko’ina, bai yadda ya rubuta sunan sa a matsayin shi ke da Levie Commercial Brokers ba. Sai ya rubuta sunan wani Ba’isira’ile David Benzaquen a madadin sa, kuma a matsayin Babban Manajan kamfani.
Shi kuma Benzaquen da ya ke tantirin ɗan harƙalla ne, sai ya samo wani kamfanin Isra’ila mai lasisin safarar makamai, wanda Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta ba shi lasisin, wato kamfanin Lavie Strategies, aka ba shi aikin hada-hadar makaman.
Tsohon ma’aikacin riƙaƙƙen ɗan kwangilar safarar makamai ne na Isra’ila, mai suna Gabi Peretz. Shi kuma Peretz abokin Shugaban Ƙasar Senegal ne, Macky Sall.
Discussion about this post