Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargaɗi jam’iyyun siyasa da magoya bayan jam’iyyu su guji tayar da fitina kan abokan adawa.
Haka kuma ya gayyaci shugabannin jam’iyyun domin ƙara jan-kunne da kuma gargaɗi.
Hakan ya biyo bayan rahotannin da su ka tabbatar da cewa wasu matasa sun kai wa magoya bayan jam’iyyar PDP hari a Kaduna, a ranar Litinin lokacin da ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar ke gangami a filin wasa na Ranchers Bees, Kaduna.
Yakubu ne da kan sa ya bayar da sanarwar yi masu gargaɗin tare kuma da gayyatar su, yayin da ya ke jawabi wurin bita da bayar da horo ga jami’an da za su horar da jami’an da za a ɗauka aikin gudanar da zaɓen 2023, wato ‘training of master trainers’, a Abuja.
An samu hargitsi a Kaduna yayin da PDP ke gangami, inda har aka ji wa wasu da dama raunuka a harin da aka kai wa magoya bayan PDP.
Hakan bai yi wa INEC daɗi ba, ganin cewa har yarjejeniyar gudanar da kamfen da kuma zaɓe cikin lumana jam’iyyun su ka sanya wa hannu a cikin Satumba.
Haka nan kuma an tabbatar da cewa an kai wa gidan ɗan takarar gwamnan Zamfara na PDP, Dauda Lawal hari a ranar Asabar. An lalata motoci bas-bas kuma aka saci wasu kayayyakin motocin.
A kan haka ne INEC ta ƙara yin gargaɗin cewa za ta ci gaba da sa-ido domin gano jam’iyyun da ke tayar da husuma.
“Mu na sane da tayar da hargitsin da wasu masu adawa su ka yi a wasu wurare. Kuma mu na sane da cewa ana danne wa wasu jam’iyyu haƙƙin yin amfani da wuraren taruka mallakar gwamnatin jiha. Hakan kuwa duk karya dokar zaɓe ta 2022 aka yi.”
Mahmood kuma ya yi kakkausan gargaɗi dangane da yadda ake amfani da kalamai zafafa na zagi da aibata ‘yan takara.
Ya ce Dokar Zaɓe ta 2022 za ta buga gudumar ta kan duk wanda ya ƙi jin bari.
2023: Abubuwan Da INEC Ta Haramta Aikatawa Lokacin Kamfen:
A farkon Satumba ne dai INEC ta fayyace wa jam’iyyu da ‘yan takara wuraren da dokar zaɓe ta haramta yin kamfen da tarukan siyasa.
Yayin da ya rage saura kwana huɗu a fara kamfen na zaɓen shugaban ƙasa, sanatoci da na mambobin majalisar tarayya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jam’iyyu da ‘yan takara cewa su guji take dokoki, musamman dokokin da hukumar ta haramta a lokacin kamfen.
Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a wancan lokacin.
Za a fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa, sanatoci da mambonin majalisar tarayya a ranar 28 ga Satumba, yayin da za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Okoye ya bayyana cewa wuraren da dokar INEC ta hana yin kamfen da tarukan siyasa sun haɗa da coci-coci, masallatai, gine-gine da ofisoshin gwamnatin tarayya, na jihohi ko ƙananan hukumomi da kuma amfani da mutum-mutumin ‘masquarade’.
Ya ce ya zama wajibi jam’iyyu da ‘yan takara su bi ƙa’idojin da Dokar INEC ta 2022, Sashe na 92 ya gindaya.
Daga cikin sharuɗɗan da Okoye ya jaddada, akwai yin hani da amfani da mutum-mutumin domin ƙara wa taron siyasa armashi, yin amfani da wuraren ibada, ofisoshin gwamnati ko gine-ginen gwamnati domin yi wa ma’aikata kamfen da sauran su.
“Sashe na 92 na Dokar Zaɓe ta 2022 ya hana rubutawa ko rera taken jam’iyya ko na ɗan takara ɗauke da kalaman zagi, cin fuska ko aibata wani ɓangaren addini, yare, ƙabila ko wani yankin jama’a.
“Ba a yarda a riƙa amfani da zage-zage a lokacin kamfen ko tarukan siyasa ba. Kuma banda kalaman da ka iya harzuƙa wani ko wasu gundun jama’a su hasala har su tayar da hargitsi. A guji amfani da yare ana cin zarafin wani yare, kuma banda shaguɓe da kalaman aibatawa da ka iya harzuƙa wasu ɗaukar doka a hannun su.
“Sashe na 3 na wannan doka ya haramta kamfen ko tarukan siyasa a wuraren ibada, ofishin ‘yan sanda, ofisoshin gwamnati da gine-ginen gwamnati. Saboda haka ba a yarda a tallata jam’iyya ko ɗan takara a waɗannan wurare ba.
“Sashe na 2(5) kuma ya haramta jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da ‘yan daba ɗauke da makamai. Kada jam’iyya ko ɗan takara ya yi amfani da wasu jami’an tsaro masu zaman kan su ɗauke da makamai a wurin kamfen, taro ko wurin zaɓe.
“Sashe na 7(a) (b) da kuma Sashe na 8 sun jaddada cewa duk wanda ya karya Sashe na 92 za a yi masa tarar naira miliyan 1 ko ɗaurin shekara 1, idan ɗan takara ne.
“Idan jam’iyya ce ta karya dokar, za a yi mata tarar naira miliyan 2. Idan ta ƙara kuma tarar naira miliyan 1.
“Wanda aka kama ya tayar da hargitsi ko ya yi amfani da makami kuma za a yi masa tarar naira 500,000 ko ɗaurin shekaru uku, ko kuma a haɗa masa duka biyun.” Inji Okoye.
Discussion about this post