Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya lula ƙasashen Turai domin yin wata ganawar hada-hadar kasuwanci.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran sa Paul Ibe ya fitar a ranar Laraba, ya ce Atiku ya tafi ne domin ganawa da wasu shugabannin wani kamfani dangane da ci bayan da aka samu sanadiyyar ɓarkewar cutar korona.
Atiku ya fice daga Najeriya kwana ɗaya bayan kallama taron Kaduna da kuma kamfen inda aka tabbatar da rahotonnin cewa wasu ɓatagari sun kai hari a wurin gangamin PDP.
Yayin da wasu ke ƙorafin cewa bai kamata Wazirin Adamawa ya fice zuwa Turai domin yin kasuwanci ko biyan wata buƙata ta shi shi kaɗai ba, a gefe ɗaya kuma wasu na yaɗa ji-ta-ji-tar cewa ya suma a wurin kamfen ne, shi ya sa aka garzaya da shi Turai bayan ya farfaɗo.
A ranar Laraba an riƙa watsa wani bidiyo inda aka nuno Atiku tare da Bukola Saraki, Daniel Bwala da Dino Melaye su na zaune ɗakin cin abinci da kuma wasu Turawa a gefe, waɗanda aka ce su ne abokan mu’amalar kasuwancin.
Dangane da harin da aka kai wurin kamfen ɗin Atiku a filin wasa na Ranchers Bees a Kaduna, da yawa sun ɗora laifin kan Gwamnatin APC a Kaduna da kuma Sanata Uba Sani ɗan takarar gwamnan Kaduna na APC.
PDP dai za ta ci gaba da kamfen a cikin wannan makon a Jihar Edo. Ba a sani ba ko Atiku zai dawo kafin lokacin, domin sanarwar fitar da ba ta bayyana kwanakin da zai yi a Turai ba.
Discussion about this post