Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu alaikum
A gaskiya da wasu Malamai suna yin amfani da nusus ire-iren wadannan, kuma su kalli hoton rayuwar Manzon Allah (SAW) shi kansa, wanda Allah ya aiko da sakon wannan addini zuwa ga bayin Allah, na irin yadda ya tafiyar da rayuwar sa wurin da’awa da kyakkyawar mu’amala da mutane, da an zauna lafiya, kuma da duniya tayi dadin zama.
To amma sai dai kash, wallahi manta wa suke yi da Annabi (SAW), su bi wata hanya ta kashin-kansu. Sai kaga Malami yana ashar, yana zage-zage, yana cin mutuncin mutane, yana maganganun batsa, yana wulakanta abun da wasu suke girmamawa, yana guluwwi da wuce-gona-da-iri, duk da sunan addini, da sunan wa’azi da sunan sunnah, da sunan da’awa. Sai aka wayi gari, maimakon su amfanar, sai suna jawo hayaniya da tsahin hankali a cikin al’ummah. Maimakon su jawo mutane, sai aka wayi gari suna korar su!
Don Allah mu kalli wadannan nusus din, da ire-iren su da suka zo cikin littafin Allah (Alkur’ani), da Sunnar Manzon Allah (SAW), wato Hadith:
“ٱدْعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلْحِكْمَةِ وَٱلْمَوْعِظَةِ ٱلْحَسَنَةِ ۖ وَجَٰدِلْهُم بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ.”
“فَبِمَا رَحْمَةٍۢ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمْ ۖ وَلَوْ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلْقَلْبِ لَٱنفَضُّواْ مِنْ حَوْلِكَ ۖ فَٱعْفُ عَنْهُمْ وَٱسْتَغْفِرْ لَهُمْ وَشَاوِرْهُمْ فِى ٱلْأَمْرِ ۖ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلْمُتَوَكِّلِينَ.”
“وَلَا تَسُبُّواْ ٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ فَيَسُبُّواْ ٱللَّهَ عَدْوًۢا بِغَيْرِ عِلْمٍۢ ۗ كَذَٰلِكَ زَيَّنَّا لِكُلِّ أُمَّةٍ عَمَلَهُمْ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّهِم مَّرْجِعُهُمْ فَيُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَعْمَلُونَ.”
“إِنَّكَ لَا تَهْدِى مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهْدِى مَن يَشَآءُ ۚ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ.”
“نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ ۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيْهِم بِجَبَّارٍۢ ۖ فَذَكِّرْ بِٱلْقُرْءَانِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ.”
“فذكر إنما أنت مذكر لست عليهم بمسيطر.”
“فَإِنْ أَعْرَضُواْ فَمَآ أَرْسَلْنَٰكَ عَلَيْهِمْ حَفِيظًا ۖ إِنْ عَلَيْكَ إِلَّا ٱلْبَلَٰغُ ۗ وَإِنَّآ إِذَآ أَذَقْنَا ٱلْإِنسَٰنَ مِنَّا رَحْمَةً فَرِحَ بِهَا ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌۢ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَإِنَّ ٱلْإِنسَٰنَ كَفُورٌ.”
“وَلَا تَسْتَوِى ٱلْحَسَنَةُ وَلَا ٱلسَّيِّئَةُ ۚ ٱدْفَعْ بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ فَإِذَا ٱلَّذِى بَيْنَكَ وَبَيْنَهُۥ عَدَٰوَةٌ كَأَنَّهُۥ وَلِىٌّ حَمِيمٌ.”
“عَنْ سَهْلِ بن سعدٍ، أنَّ النَّبيَّ ﷺ قَالَ لِعَليًّ: فو اللَّهِ لأنْ يهْدِيَ اللَّه بِكَ رجُلًا واحِدًا خَيْرٌ لكَ من حُمْرِ النَّعم.” [متفقٌ عليهِ]
“ليس المؤمن بالطعان ولا اللعان ولا الفاحش ولا البذيء.” [رواه الترمذي والحاكم وصححه الألباني]
عن أنس – رضي الله عنه – قال: قال رسول الله – صلى الله عليه وسلم: “يسِّروا ولا تعسِّروا، وبشِّروا ولا تنفِّروا.” [متفق عليه]
Annabi (SAW) bai taba yin wa’azi ko da’awa yana zagi ko ashar ba, bai taba fitowa fili ya ayyana wani ko wasu a matsayin kafirai, batattu, halakakku, ko fasikai ba. Bai taba raina manyan wasu, ko ya zagi abunda suke girmamawa ba!
Kullun kokari yake yi ya jawo mutane cikin addini, ba wai ya kore su ba. Kokari yake yi mutane su shiryu, su gyara munanan halayen su da dabi’un su marasa kyawo, ba wai so yake yi su bata ko su halaka su shiga wuta ba!
Annabi (SAW) yayi hakuri matuka, shi yasa yaci nasara, nasarar da duk duniya ta shaida, kai hatta makiyansa sun yarda kuma sun amince yaci nasara!
Jawo mutane ake yi da magana mai dadi, da wa’azi mai kyawo. Ba yadda za’a yi ka zama kamar kana yakar mutane, ko kana fada da su, har ya kasance sun saurare ka, ko su amfana da wa’azin ka.
Ka gamsar da mutum cewa abun da kake akai shine daidai, kuma shine gaskiya ta hanya mai kyawo. Sannan ka gamsar da shi cewa abun da yake akai kuskure ne, ba daidai bane, ta hanya mai kyawo, ba tare da ka zage shi ko ka taba mutuncin sa ba.
Musuluncin da yazo ya gyara duniya da dukkanin mutanen da ke cikin ta, amma saboda halayen mu da dabi’un mu, sai aka wayi gari ana kallon ba abun da Musulunci ya kawo idan ba hayaniya da tashin hankali ba!
Shi yasa har kullun, muke ta kiran mutane akan cewa kar su yi la’akari da halaye da dabi’un ko wane mai da’awa, a’a, maimakon hakan, suyi kokari su karanci hoton rayuwar Manzon Allah (SAW), a hannun malaman Allah. Idan sunyi haka, tabbas zasu zauna lafiya kuma su fahimci addini!
Sannan tarihi ya karantar da mu cewa, Sahabban Annabi (SAW), sun kasance suna gamsar da mutane, su shigar da mutane cikin addinin Musulunci, da kyawawan halayensu, da dabi’unsu nagari, da kuma kyakkyawar mu’amalar su ga mutane, ba tare da sun ja aya ko hadisi ba. To amma mu a yau fa?
Allah ya sawwake, amin.
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau. Lahadi, 23/10/2022. 08038289761.
Discussion about this post