Ɗan takarar shugabancin Najeriya a APC, Bola Tinubu, ya sha alwashin cewa zai ci gaba da bijiro da ayyukan raya ƙasa daga inda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tsaya.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a wuri Taron Bunƙasa Tattalin Arziki Da Zuba Jari, a Kaduna, a ranar Asabar.
Ya ce gwamnatin Buhari ta yi ayyukan ci gaba, saboda haka shi ma zai ɗora wajen samar da yanayin inganta kasuwanci da zuba jari, bunƙasa cinikayya da inganta ayyukan ci gaba.
Ya ce zai bijiro da yin amfani da fasahar zamani wajen hana zurarewar da aljihun gwamnati ke yi, kuma zai inganta tsaro.
Tinubu ya ce ko tantama ba ya yi, APC ce za ta lashe zaɓen 2023.
“Za mu daƙile matsalar tsaro. Ba za mu bar kowane yanki a hannun ‘yan bindiga ba ko ‘yan ta’adda.
“Za a inganta dabarun faɗa kan sojojin Najeriya ta hanyar inganta ayyukan su, kuma ko dai ba mu kakkaɓe matsalar tsaro baki ɗayan ta ba, to za mu daƙile ta, ta yadda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba za su sake yin tasiri ba.
Ya yi kiran da a zaɓi APC domin babu wata jam”iyyar da ta kai ta cancanta. Ya ce bambancin su kamar wanda ya shuka masara ne da wanda ya shuka dawa.
Da ya koma kan Gwamna Nasiru El-Rufai, ya roƙe shi kada ya yi ritaya daga gwamnati da siyasa bayan ya kammala wa’adin sa a 2023.
Shi kuwa tsohon Sarkin Kano, kuma Khalifan Tijjnaniya a yanzu, Muhammadu Sanusi II, ya ce aikin gyaran Najeriya ba wasa ba ne. “Duk wanda ya ce maka zai gyara Najeriya da ya hau mulki a cikin sauƙi, to ko dai maƙaryaci ne, ko kuwa bai san abin da ke damun Najeriya ba.
Discussion about this post