Darektan hulɗa da jama’a da sabbin kafafen yaɗa labarai na kwamitin kamfen ɗin Bola Tinubun APC, Femi Fani-Kayode ya maida wa Godwin Obasake kakkausar martani.
Fani-Kayode ya ce ” Korafin Obaseki karauniya ce da hayagaga kawai, amma wai ace Atiku ne zai tallata, ai babu mayaudari irin Atiku a siyasar Najeriya.
” Atiku ne ya hargitsa, ya dagula ya yi rugurugu da siyasar rikon amana a Najeriya saboda tsantsagwarar son kai da yaudara irin ta sa.
” Atiku ne ya kawo kwamacalar da aka samu a lokacin mulkin Obasanjo, daga 1999 zuwa 2007. Shine ya dagula komai, ya ruruta cin amana da yaudara karara a tafiyar siyasar Najeriya.
” Bayan karya alkawarin da PDP ta ɗauka na tsarin Ƙarba-Ƙarba, Atiku ne kan gaba wajen yaki da takarar Jonathan a 2019 bayan ya yaudare shi.
Korafin Obasaki
Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya hargaɗi ƴan Najeriya kada su kuskura su zaɓi APC a zaɓe mai zuwa domin yin haka ganganci ne na gasken gaske.
” Ni fa a ganina duk wanda zai zaɓi Tinubu, yana buƙatar a duba ƙwaƙwalwar sa, domin lallai akwai zautuwa, ko taɓuwa, ko tantama ba na yi. Mai cikakken hankali da lafiya ba zai zaɓi Tinubu ko APC a 2023 sai dai fa duk dan ya na so komai ya sake dagulewa ne a wannan ƙasar.
” Allah dai ya kyauta, amma ace tsautsayi ya kai ga APC ta sake kafa gwamnati a Ƙasar nan, shi kenan mun banu mun lalace, domin ƙasar rugujewa za ta yi idan aka yi la’akari da irin ruɗani da birkita kasar da APC ta yi yanzu.
Obaseki ya kara da cewa ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ne kawai zai yi nasara kowa ya kasa barci don murna domin kuwa Karafila sarkin aiki ne ya yi nasara.
” Kai bari in ƙara tabbatar muku yau ku sani, tsantsagwaran bashin da ake bin Najeriya yanzu ya kai naira Tiriliyan 60. Ina zamu saka kan mu idan APC ta sake zarcewa ay shikenan kuma kasa Najeriya zai zama tarihi kenan, domin rugujewa zata yi.
Obaseki yayi waɗannan kalamai ne a jawabin sa lokacin da yake kaddamar da kwamitin kamfen ɗin PDP a garin Benin, Babban birnin jihar Edo a farkon wannan makon.
Discussion about this post