Jam’iyyar APC ta kafa Reshen Mata na Rundunar Kamfen ɗin Tinubu-Shettima 2023, inda aka naɗa Uwargidan Shugaban Ƙasa, A’isha Buhari Shugabar Kamfen ta Mata ta Ƙasa.
Matar Bola Tinubu, wato Remi Tinubu ce ita da Nana Shettima, uwargidan Kashim Shettima su ma su na cikin shugabanni. A’isha Buhari ce Babbar Shugabar Kamfen baki daya.
Asabe Villita, wata tsohuwar ‘yar majalisar tarayya daga Jihar Barno ce aka naɗa kodinatan kamfen ta mata ta ƙasa, ita Lauretta Onochie kuma mataimakiyar ta.
Sai dai kuma babu sunan uwargidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Dolapo Osinbajo a cikin rundunar matan kamfen ɗin, wanda Rinsola Abiola ta fitar da sunayen a ranar Asabar, a Abuja.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda babu sunan Osinbajo cikin rundunar kamfen ta Tinubu, wadda daga baya APC ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ce kada a saka shi, domin ya riƙa tsayawa ya na gudanar da mulki, tunda Buhari ne Kwamandan Kamfen baki ɗaya.
Osinbajo dai ƙin janye wa Tinubu ya yi a lokacin zaɓen fidda-gwani, inda ya sha kaye.
Ya yi Kwamishinan Shari’a a ƙarƙashin Tinubu a Jihar Legas, lokacin da Tinubu ke gwamna.
An kuma haƙƙaƙe cewa Tinubu ne ya bayar da sunan sa Buhari ya ɗauke shi mataimaki a takarar 2015.
Har yanzu dai APC na fama da ƙalli-ƙalallar da ta dabaibaye jam’iyyar dangane da batun tikitin Muslim-Muslim.
A ƙarƙashin wannan rundunar kamfen, an naɗa matan kowane gwamna ita ce kodinatar kamfen ta jihar da mijin ta ke gwamna na APC.
Zainab Bagudu ce Kodinatar Shiyyar Arewa maso Yamma, Fatimata Zulum ta Arewa maso Gabas, Olufolake Abdulrasaq ta Arewa ta Tsakiya, sai Claudian Sanwo-Olu ta Arewa maso Yamma. Yayin da Chioma Uzodinma ta Kudu maso Gabas, ita kuma Linda Ayade ta Kudu maso Kudu.
Wato su ne matan gwamnonin Kebbi, Barno, Kwara, Legas, Imo da Kuros Riba.
Sanarwar ta ce dukkan matan ministoci, sanatoci mata da ministoci mata na APC duk mambobin kwamitin kamfen ɗin mata ɗin ne.
Discussion about this post