An cire tsohon Osun, Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola daga cikin Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu na jam’iyyar APC.
Haka kuma shi ma tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Chimaroke Nnamani da tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, sai kuma Kassim Afegbua duk an cire su daga rundunar yaƙin.
An tsame sunayen su daga cikin sunayen ‘yan kamfen ɗin da aka yi wa garambawul.
Sakataren Kamfen ɗin TInubu da Shettima, Iyiola Omisore ne ya fitar da sabbin sunayen bayan garambawul ɗin da aka yi, biyo bayan korafe-ƙorafen da gwamnonin APC da wasu su ka riƙa yi cewa ba a yi masu daidai wajen haɗa gayyar yaƙin ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Gwamnonin APC su ka yi barazanar yi wa rundunar kamfen ɗin TInubu ƙafar-ungulu, saboda ba a saka sunayen makusantan su cikin tafiyar ba.
Haka shi ma Shugaban APC Abdulalhi Adamu ya rubuta wa Tinubu wasiƙar ƙorafin cewa an watsar da wasu shugabannin jam’iyyar wajen haɗa rundunar. Amma dai daga baya APC ta ce ba ta rubuta wa Tinubu wasiƙar ba.
An zargi Gwamna Abubakar Bagudu da kuma Babban Daraktan Kamfen Gwamna Simon Lalong da cukurkuɗa sunayen su ka tsarma sunayen wasu da jiga-jigan APC su ke so a saka.
Wannan ƙalli-ƙalalla ce ta haifar da saɓanin da tilas APC ta dakatar da fara kamfen ɗin shugaban ƙasa.
A tsohon jerin sunayen dai akwai Aregbesola, Nnamani da Kalu. Amma a sabon jerin sunayen da Sakataren APC, Omisore ya fitar ranar Laraba, babu sunayen su.
An samu saɓani da Aregbesola da Tinubu a kan zaɓen gwamnan Osun da aka yi watannin baya.
Aregbesola bai goyi bayan Gwamna Gboyega Oyetola ya yi tazarce ba, wanda ɗan uwan Tinubu ne.
Lamarin ya yi munin da har Aregbesola ya riƙa caccakar Tinubu saboda katsalandan ɗin da ya ce Tinubu ɗin ke yi a siyasar Osun.
Shi kuma Nnamani dama Sanata ne a yanzu na PDP, wanda dama tsarma sunan sa da aka yi ya jawo ruɗani da ce-ce-ku-ce.
Idan ba a manta ba, Kalu ya tsaya takarar fidda-gwanin APC a zaɓen shugaban ƙasa, amma da ya ga ba a bar wa Kudu maso Gabas takara ba, sai ya nuna goyon bayan sa ƙarara ga Sanata Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa.
Sabbin sunayen da aka ƙara sun haɗa da Kakakin Majalisun Dokoki na jihohi da mataimakan su da masu riƙe da gafaka a majalisun. Sai kuma sunayen tsoffin Kakakin Majalisar Dokokin Jihohi na APC da shugabannin jam’iyyar APC na jiha, ‘yan Majalisar Tarayya da na jihohi na APC.
Discussion about this post