Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana wa masu zuba jari a jihar Kaduna cewa kada hankalinsu ya tashi ko kaɗan bayan wa’adin mulkin sa ya cika a 2023.
” Ina so in tabbatar muku cewa jihar Kaduna zai cigaba da samun cigaba da ayyukan raya kasa fiye da yadda yake a yanzu domin abu uku ne kacal za su canja a jihar Kaduna idan wa’adin mulki na ya cika Uba Sani ya ɗare kujerar mulki a jihar Kaduna.
” Abu na farko da zai canja shine faskar gwamna, wato El-Rufai, na biyu shine fuskokin wasu tsofaffin ma’aikatan gwamnati sai kuma wasu sauye-sauye da zai bijiro da su waɗanda za su ɗau saiti da abinda muka yi a yanzu.
” Uba zai cigaba daga inda muka tsaya, zai kuma kawo sauyi ga wasu da muke akai, waɗanda yake ganin ba mu yi su daidai ba, domin ba duka abinda muka yi bane daidai, mu mutane kuma za mu iya yin kuskure, duk zai gyara su idan ya ɗare gwamnati.
A dalilin haka El-Rufai ya tabbatar wa masu saka jari a jihar Kaduna da su kwantar da hankulan su domin jarin su ba zasu salwanta ba.
Ɗan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a lokacin da yake jawabi a wurin taron ya ce kyan ɗa ya gaji uban sa.
” Baban abinda shugaba zai yi idan ya son ya girbi abinda ya shuka, kuma jama’a su mori haka ko bayan bashi shine ya goya magaji. Uba Sani magajin kwarai ne.
Discussion about this post