Idan ba a manta ba dan takarar shugaban Kasa na APC Bola Tinubu a wajen kaddamar da Kundin tsarin mulkin sa inda ya bayyana wasu abubuwa da zai kaddamar da kuma zai aiwatar idan ya zama shugaban kasa a 2023, an gano cewa mafi yawa daga cikin ayyukan da ya ce zai aiwatar duk APC ta fade su a 2015.
Kamar dai yadda suke kunshe a cikin kundin alkawuran da APC ta dauka wa ‘yan Najeriya a can baya shima Tinubu ya ce zai farfado da tattalin arzikin kasa, zai farfado da masakun Kaduna, sannan zai kawo karshen biyan tallafin kudin mai da gwamnati ke biya.
Buhari ya ce shi da kan sa zai jagoranci kamfen din Tinubu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tabbas shine da kansa zai jagoranci zirga-zirgan kamfen ɗin Bola Tinubu.
Buhari ya ce ” Ni da kai na zan jagoranci wannan tafiya, kuma ina so n n tabbatar muku cewa wannan tafiya ba ta wasa bace, da ƙarfin mu za mu fito don samun nasara.
” Tinubu mutum ne mai jini a jika, sannan gogarman siyasa a Najeriya. Idan kana so ka tabbatar da haka ka garzaya Legas ka ga irin shimfiɗar da yayi mata tun daga 1999 zuwa yanzu.
” Wannan ma kawai ya ishe ka yanke wa kanka hukunci cewa zaɓin da APC ta yi na Tinubu ɗan takarar shugaban kasar ta zaɓi ne mai kyau.
Buhari ya ƙara da cewa dole jam’iyyar sa ta APC ta dunƙule wuri ɗaya ta tunkari wannan kalubale gadagadan domin samun nasara.
” APC ba za yi wasa ba, ba za mu bari akalar ta canja ba dole mu tabbatar mulki ta cigaba karkashin APC har bayan 2023.
A nashi jawabin, gogan tafiyan Bola Tinubu ya yi alƙawarin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar bunkasa masana’antu da farfaɗo da waɗanda suka mutu.
A cikin wata littafi wanda aka kaddamar a wurin taron mai shafi 80, da kuma ke kunshe da yadda gwamnatin sa idan ya yi nasara za ta gudanar da ayyukan ci gabanta , Tunubu ya ce zai maida hankali matuka ga harkar samar da tsaro a kasar nan.
Discussion about this post