Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa dakarun Najeriya dake aikin samar da tsaro a dazukan da suka yi iyaka titin Kaduna-Abuja sun gama da wasu ƴan bindiga da suka bi su har cikin ƙungurmin daji suka yi fatafata da su.
Aruwan ya ce a wannan karon ba a saurara musu ba, dakarun Najeriya sun bisu ne har can cikin daji inda suke ɓoye suka yi dagadaga da su.
Bayan haka kuma waɗan da ke aiki a yankin dazukan da suka yi iyaka da karamar Hukumar Chikun ma sun samu nasara akan wasu ƴan bindigan inda suka ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su.
Maharan sun arce sun bar mutanen da suka yi garkuwa da su a lokacin da suka ji diran jami’an tsaro a wannan dajin.
Karamar hukumar Chikun na daga cikin wuraren da ‘yan ta’adda ke yawan kai wa hare-hare a jihar Kaduna.
Aruwan ya ce tuni har an mika waɗanda aka ceto ga ƴan uwan su.
Discussion about this post