A cikin daren Talata, da misalin karfe goma na dare, barayi suka shiga Unguwar Tsunami, da ke cikin garin Gusau, Jihar Zamfara, suka yi awon gaba da mutane hudu.
Kamar yadda majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA, cikin mutanen akwai matar aure da budurwa wadda saura kwana bakwai ayi mata aure, duk sun tafi dasu.
Babban malami, Murtadha Gusau wanda ya tabbatar wa jaridar nan da aukuwar abinda ya roki jama’a da a taya su addu’a, ” Allah ya kubutar da su, da dukkanin sauran bayin Allah da suke hannun barayi; kuma muyi ta istighfari, da tuba, da komawa zuwa ga Allah, da yawaita sadaka, da addu’a da rokon Allah ya kawo muna karshen wannan jarabawa, a jihar mu ta Zamfara, da sauran jihohin Nigeria, da Nigeria baki daya, amin”.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴan bindiga a tsawon shekaru shidan wannan gwamnati.
Sai dai kuma shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa nan da karshen wannan shekara ta 2022, gwamnati sa za ta gama da ƴan bindiga gaba ɗaya.
Ministan Ayyukan cikin gida, Rauf Aregbesola ya tabbatar da haka a cikin wannan mako inda ya ke cewa gwamnati mai ci za ka gama da ƴan bindiga da duka ƴan ta’adda da suka addabi Najeriya.
Discussion about this post