‘Yan sandan musamman na konsitabul sun fito kan titi sun yi zanga-zanga ta lumana a ranar Laraba, saboda takaicin rashin biyan su albashin watanni 18.
‘Yan sandan sun yi taron gangamin fara zanga-zangar ne a shatale-talen Oke-Fia, daga can su ka nausa ta cikin unguwannin Alekunwodo har cikin unguwar Olaiya a garin Osogbo, babban birnin Jihar Osun.
Sun yi wannan jerin gwanon zanga-zangar lumana su na sanye da kayan ‘yan sanda, yawancin su kuma na ɗauke da kwalayen da aka yi wa rubutu kamar haka, “A biya mu yanzu”, “Yunwa na kashe mu”, “Yunwa ta kwantar da mu”, “Watanni 18 ba a biya mu ko sisi ba”, “Yan Okada na kwana da matan mu saboda rashin albashi.”
Wasu masu zanga-zanga sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa “har ƙwacen matayen su ake yi masu saboda sun kasa ciyar da su.”
Konsitabul ɗin sun ce sun sadaukar da rayuwar su wajen aiki duk da cewa an daɗe ba a biyan su.
Wani mai suna Tijani Adewale ya faɗa wa wakilin mu a fusace cewa abokan aikin sa uku su ka mutu a wurin aiki.
“Ga mu da kishin aiki duk da cewa ba a biyan mu albashin mu ko sisi. Saboda an kasa biyan mu alawus ɗin haƙƙin mu, har masu Keke NAPEP da ‘yan Okada ke mana ƙwacen matayen mu, tunda ba mu iya ciyar da su.” Inji Adewale.
Ya ce sun je duk wuraren da su ka kamata su kai ƙorafi, amma a banza.
Da yawa daga cikin su sun ce su na bin albashi ko alawus na watanni 18.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Osun Adewale Olokode, ya yi masu jawabi kuma ya yi kira da su aika da koken su inda ya dace, maimakon su fito zanga-zanga.
“Gaskiya kun zubar wa ‘yan sanda mutunci da darajar su. Kamata ya yi ku kai kuka inda ya dace, ba wai ku fito zanga-zanga ba.” Inji shi.
Discussion about this post