Ɗan takaran gwamnan jihar Kano na jam’iyyar ADP Shaaban Sharaɗa ya bayyana cewa idan ya zama gwamna zai baiwa kananan hukumomin Kano ƴancin kansu.
Sharaɗa ya faɗi wa dubban magoya bayan sa a filin wasa na Sani Abacha dake Kano cewa gwamnatinsa za ta kawo karshen satar kuɗi da ake yi musamman na kananan hukumomi ta hanyar basu ƴancin kansu.
” Zan baiwa kananan hukumomin Kano ƴancin kansu kowace karamar hukuma za ta rika samun kuɗaɗen ta kaitsaye ta kuma aiwatar da ayyukan ta da kanta ba ta hanyar asusu da ake musu kwange ba kamar yadda gwamnati maici ke yi.
” Bayan haka zan gina cibiyar kiwon lafiya 484 a fadin jihar domin kiwon lafiyar mutanen mu.
Idan ba a manta ba Sharaɗa ya canja sheka daga jam’iyyar APC zuwa ADP batan ya yi zargin an yi masa murɗiya a zaɓen ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen fidda gwani na gwamna.
Daga nan sai ya koma jam’iyyar ADP.
Honorabul Shaaban Sharada na wakiltar Kano Municipal a majalisar Wakilai ta Tarayya.
Mataimakin gwamnan jihar Borno Nasiru Gawuna ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Kano. Shine mataimakin gwamna.
Sharaɗa da fafata da Abba Gidagida na jam’iyyar NNPP, Gawuna na APC da Mohammed Abacha na PDP a zaben 2023.
Discussion about this post