Mazauna ƙauyuka da garuruwa 14 ne su ka yi karo-karon tara naira miliyan 19 da ‘gudummawar’ kwale-kwale ga ‘yan ta’addar da su ka buwayi yankin Anka da Bukkuyum, matsayin harajin daina kai masu hare-hare da kuma sulhun kare su
Wani ɗan jarida mai suna Yusuf Anka ne wanda ɗan asalin yankin da su ka biya harajin ne ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa ‘yan yankin sa da yawa an tilasta masu biyan harajin na tilas.
Ya ce ‘yan bindigar sun ƙaƙaba wa garuruwan harajin ne kafin faɗuwar ruwan shuka.
Ya ce ‘yan ta’addar sun nemi a biya su kuɗaɗen domin su ƙyale mazauna yankunan su yi noma a farkon zubar ruwan shuka.
Anka ya ce mazauna yankunan ba su da wani zaɓi, tilas su ka biya harajin domin kada ‘yan ta’addar su fusata su auka masu a lokutan da su ke noma a gonakin su da kuma gudun tarwatsa ƙauyukan su.
“Ƙauyukan duk a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Anka su ke, kuma ƙaƙaba masu harajin aka yi. Wasu sun biya tun watanni biyu da su ka gabata, wasu kuma yanzu su ke ta kai wa ‘yan ta’adda na su harajin da su ka tattara. Amma dai zuwa yanzu an biya naira miliyan 19 da kuwa kwale-kwale.” Inji Anka.
Anka shi ne ya yi bincike mai zurfi a kan ‘yan ta’addar Zamfara, shi ne ma ya yi bidiyon da BBC ta nuna, wato “The Bandits Warlords of Zamfara.”
Ya ce mutanen ƙauyen ‘Yar Sabaya su ka haɗa kuɗi, su ka sai wa ‘yan bindiga kwale-kwale. Garin Anka kewaye ya ke da kogi biyu da wasu ƙananan ƙoramu.
“Yan bindiga sun riƙa bin ƙauyuka su na cewa kowane ƙauye ya haɗo masu kuɗaɗen da su ka yanka masu idan har su na so a bari su yi nema.
“Kuma ba wannan ne karo na farko ba da aka tilasta masu biyan haraji ga ‘yan ta’adda ba.” Inji Anka.
Ya ce ƙauyen Jargaɓa sun haɗa Naira miliyan 1.6 na Birnin Doki kuwa naira miliyan 1, sai kuma mutanen ƙauyen Tangaram sun tara naira miliyan 1.5, amma daga baya sun ƙara, kuɗin na su ya kai naira miliyan 2.5. Sai kuma an karɓi Naira miliyan 1.5 daga mutanen ƙauyen Jarkuka, Tuntuja kuma Naira 500,000.
“An karɓi Naira miliyan 1 daga mazauna Tudun Magaji sun biya Naira biliyan biyu, sai Kadaddaba, naira 820,000, sai Tudun Kudaku naira 950,000, Gargam naira miliyan ɗaya, sai Kwanar Make 900,000, ‘Yartumaki naira miliyan ɗaya, Baiwar Daji Naira miliyan 1.7, Tungar Liman naira miliyan 6, sai Makakari naira 430,000.00.
Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu bai ɗauki kiran wayar da wakilin mu ya yi masa ba, domin jin ta bayin sa.
Discussion about this post