Hukumar Bunƙasa Ilmi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta ce Yara Ƙananan da ba su zuwa makaranta a Najeriya sun kai miliyan 20.
UNESCO ta ce aƙalla akwai yara miliyan 244 da su ka kama daga shekaru 6 zuwa 18 a duniya waɗanda ba su zuwa makaranta.
Ƙididdigar ta nuna Indiya, Najeriya da Pakistan ne su ka fi yawan yaran da ba su zuwa makaranta.
Adadin Najeriya ya ƙaru daga yara miliyan 10.5 zuwa miliyan 15 a shekaru goma da su ka gabata. Sai dai kuma a yanzu adadin a Najeriya ya ƙaru zuwa miliyan 20 saboda matsalar tsaro.
UNESCO ta fitar da wannan ƙididdiga a ranar Alhamis, inda a ranar ta aiko wa PREMIUM TIMES adadin ƙididdigar ta hannun Dafalia Dimitra, ƙwararre a harkar jarida da ke tare da GEM gwanayen ƙididdigar ya nuna ƙasashen yankin Saharar Afrika ne su ka fi ɗimbin yawan yaran da ba su zuwa makaranta da su ka kai har miliyan 98.
Rahoton ya ce kuma a wannan nahiya ce kaɗai yawan waɗanda ba su zuwa makaranta ke fin yawan masu zuwa makaranta.
“Yankin Asiya ta tsakiya da ta Kudu ne na biyu da yawan yara har miliyan 85.
Ƙasashe uku da su ka fi yawan yaran da ba su damu da zuwa makaranta, su ne Indiya, Najeriya da Pakistan.
Daraktan Cibiyar Ƙididdiga ta UNESCO, Sylvia Montoya ce ta tabbatar da haka bayan ta fitar da ƙididdigar.
A Najeriya dai Boko Haram da ‘yan bindiga sun haifar da matsalar ɗimbin ƙananan yara da ba su da ba su zuwa makaranta.
Discussion about this post