‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da dagargazar Uwargidan Shugaban Ƙasa, A’isha Buhari, saboda watsa hotunan bukin kammala digiri na surukar ta, Zahra Buhari da ta yi.
A’isha Buhari dai ƙilu ta ja mata bau ce saboda watsa hotunan matar ɗan ta Yusuf Buhari, wato Zahra Buhari.
Haushin da ‘yan Najeriya ke ji shi ne saboda ta nuna muryar kammala digiri ɗin da Zahra ta je ta yi a jami’ar ƙasar waje, a lokacin da Gwamnatin Buhari ta kasa magance yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ((ASUU), wanda ya yi sanadiyyar ɗaliban Najeriya zaune gida tsawon watanni bakwai.
An riƙa nuna cewa “wannan bai dace ba”, kuma ƙoƙarin jin ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran uwargidan Buhari ɗin mai suna Aliyu Abdullahi bai yi nasara ba, saboda an kasa samun wayoyin sa a lokacin da aka kira shi.
A ranar Talata ce dai A’isha Buhari ta watsa hotunan a shafin ta na Facebook, inda ya ke taya Zahra murna ta samu babban sakamako mafi daraja (First Class Honours) a Fannin Kimiyyar Zanen Gidaje.
Yayin da Aisha ta taya ta murna, amma ba ta ambaci sunan jami’ar da matar ta Yusuf Buhari ta kammala ba.
Haka kuma a ranar Laraba A’isha Buhari ta buga hoton Zahra tare da Buhari a shafin ta na Facebook, inda ta bayyana cewa ” Zahra ta na cikin tawagar ‘yan rakiya ta zuwa Taron Majalisar Ɗinkin Duniya.”
Aƙalla ‘ya’yan Buhari biyar ne su ka yi karatu a jami’o’in kashashen Turai. Nana-Hadiza, Safinatu, Halima, Zahra da Yusuf Buhari duk a Turai su ka yi karatu.
Jama’a da dama sun riƙa caccakar A’isha Buhari ana nuna rashin dacewar abin da ta aikata.
Ɗan taratsi Deji Adeyanju cewa ya yi Buhari ya damfari jama’a a 2015, “ya’yan Najeriya na zaune gida watanni tara saboda yajin aikin ASUU, su kuma su na murna da bukin ‘yar su ta kallama jami’a a Ingila.”
Discussion about this post