Wani dalibin Jami’ar Usmanu Danfodiyo UDUS dake jihar Sokoto Usman Abubakar-Rimi ya fara sana’ar siyar da indomie da kwai a dalilin yajin aikin ASUU da yaki ci yaki cinyewa a kasar nan.
Abubakar-Rimi wanda ke shekarar sa ta karshe a karatun likitanci da ya ke yi ya ce zaman gida da ya ishe shi ya sa ya fara sana’ar saida da abinci.
” A dalilin wannan sana’a da nake yi yanzu na tara kuɗi sosai. Baya ga indomi da kwai da nake yi a shagon ina kuma siyar da masa, farfesu, shinkafa da wake da tsire sannan kuma akwai POS da na buɗe duk a cikin shagon.
“Farantin abinci kowace iri a shago na naira 200 ne amma farashin na iya karuwa bisa ga abinda mutum ke so a kara masa a cikin abincin.
Abubakar-Rimi ya ce baya ga wannan shago da ya bude a cikin garin Sokoto yana kuma da wani shagon da yake siyar da kayan sawa na maza da mata a titin Fodio.
A karshe ya yi kira ga sauran ɗalibai su rungumi sana’a maimakon zaman gida da suke yi .
Discussion about this post