Wani barawo da rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara suka kama ya bayyana yadda ya shahara wajen sace wa mutane kudi da idan sun ciro daga banki.
Kakakin rundunar Muhammad Shehu ya bayyana cewa sun kama Umar Usman dan shekara 39 kuma ɗan kungiyar fashi da suka shahara wajen sace wa mutane kudi idan suka ƙarbo daga banki da wuraren da ake cire
kuɗi.
Usman ya bayyana wa jami’an tsaro cewa kungiyar su na ƴan fashi da sane na tabargazarsu a jihohin Borno, Bauchi, Kebbi da Sokoto.
Shehu ya ce bayanin da Usman ya yi ya taimaka wa jami’an tsaro wajen gano naira miliyan 3,500,000 kudin wani Nura Shinkafi dake aiki a ofishin zuba jari dake Gusau a jihar Zamfara.
“Shinkafi ya ce barayin sun fasa gilashin kofar motar sa kiran Peugeot 406 inda suka sace jakarsa dake dauke da komfutansa Kiran HP mai lanban CND0515RPN da kudinsa naira 250,000.
“Sauran kayan dake cikin jakan da aka sace sun hada da katin shaida na ofishin zuba jari na jihar Zamfara da tsaban kudi har naira 3,500,000.
Ya ce bayan rundunar ta yi nasaran kama Usman rundunar na kokarin kama wani barawo mai suna Abdul mazaunin Zaria, jihar Kaduna da ya tsere.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kolo Yusuf ya yi kira ga mutane da su rika yin taka tsantsan a duk lokacin da suke je cirar kudi a banki ko a wajen masu POS domin guje wa fadawa hannun ‘yan fashi irin haka.
Yusuf ya kuma kara yin kira ga mutane da su kai karar duk wani wanda basu yadda da shi ba ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Za a kai Usman kotu idan rundunar ta kammala bincike akai.
Bayan haka kuma Ƴan sandan jihar sun yi nasarar cafke wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Isiyaku Babangida Mai shekara 31 a jihar.
Shehu ya ce ‘yan sandan sun kama Babangida bayan sun samu bayanan sirri kan ayyukan sa.
Ya ce sun kama dan bindigan yayin da yake shirin kai wa kauyukan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum hari.
Discussion about this post