Hukumar NDLEA reshen jihar Kano ta kama kwalaben’ Akurkura’ 26,600 a jihar.
Hukumar ta kama Qasim Ademola mai shekaru 39 ranar 15 ga Satumba a hanyar Zaria zuwa Kano a daidai gadar Tamburawa.
Ademola dan asalin karamar hukumar Akinyele ne dake jihar Oyo sannan bayan gudanar da bincike hukumar ta kama wasu mutum uku dake harƙallar wannan magani na Kurkura.
NDLEA ta ce ta cafke Ademola yayin da yake hanyar sa ta zuwa siyar da kwayan a jihohin Arewacin Kasar nan.
Menene kurkura
kurkura magani ne da ake kurbarsa a kuskure baki. Shikenan, ” Amma kuma fa daga lokacin da ka rike shi a cikin bakinka zai fara aiki.
Wani abu da ya zame wa mutanen Najeriya musamman a yankin Arewacin Najeriya annoba inda babu yara matasa, harta magidanta, malamai, ‘yan kasuwa, direbobi da sauransu kowa yana amfani da wannan magani ‘Kurkura’.
Anfi siyar da wannan magani a shagunan siyar da magungunan gargajiya, wasu da dama da ake kira ‘Islamic Chemist’ wanda ale dura ta a cikin dan Kwalba karami.
Maganin an ce wai yana maganin kowani irin cuta sannan har an yi mata lakabi da suna ‘Antibiotics’
Duk mai shan maganin zai rika cewa wai magani ne da yake masa aiki wajen magance cutar sanyi, basir, amosani, da dai duk wata cuta dake damun mutum.
Babbar abin tashin hankali ga wannan magani ‘Kurkura’ shine daga ka fara yin shi shikenan ka kamu. Baka iya rayuwa sai da shi. A kowani hali kake za ka bukaci kurkura domin ka rayu
Abin takaicin shine maganin ya yi ajalin wasu da dama da suka fara amfani da maganin sannan likitoci sun tabbatar cewa maganin na cutar da lafiyar mutum wanda sai bayan an yi shekaru ake ganin illar sa.
Discussion about this post