Mazauna kauyen Ruwan Jema dake karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 18 a masallacin Juma’a.
Majiya da dama daga kauyen sun bayyana cewa maharan sun afka kauyen da misalin karfe 1 na rana a lokacin da masallata na shirin yin sallar juma’a.
Ana zargin cewa ‘yan bindigan da syka kai harin yaran Dogo Gide ko na Shadari ne dake zama a
Wani dan asalin karamar hukumar Bukkuyum Abdullahi Salisu ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun shigo kauyen yayin da ake shirin fara sallar Juma’a inda suka shigo masallacin suka yi ian mai uwa dawabi.
“Maharan sun shigo kauyen akan babura inda suka nufi masallaci kai tsaye. Da mutane suka ji zuwa
su sai suka rugo waje, sai dai kuma duk wanda ya fito waje daga masallacin ƴan bindigan sun harbe shi.
Wani basarake da baya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya ce mazaunan kauyen da dama da suka ji rauni na kwance a babban asibitin Bukkuyum.
Ya ce mutum hudu da suka ji mummunar rauni a jikinsu na asibitin Usman Danfodio dake Sokoto likitoci na duba su.
“Akwai mutum sama da 10 da suka ji rauni dake asibitin Bukkuyum amma da safiyar nan na ji lokacin da likita ya aika da wasu mutum hudu zuwa asibitin Usman Danfodio dake Sokoto.
Wani mazaunin Bukkuyum, Abubakar Usman ya ce akwai yiwuwar mutanen da suka mutu a sanadiyyar harin za su fi 18.
Usman ya ce rundunar ƴan sanda da sojojin jihar sun hada hannu domin Samar da tsaro a kauyen.
Discussion about this post