Masallata da yawa ne ƴan bindiga suka sace a masallacin Juma’a dake Zugu, Karamar hukumar Bukkuyum, jihar Zamfara.
Majiya ta shaida mana cewa maharan sun kwashe mutane ne a daidai ana wa’azin farko kafin Liman ya iso.
Yasir Sahabi ya shaida cewa shima Allah ne yayi ba za a tafi da shi ba, domin bai tafi masallaci da wuri kamar yadda ya saba ba.
” Abokina Junaidu na daga cikin waɗanda aka tafi da domin shi ya tafi masallaci da wuri. Kuma nima haka nake yi sai dai wannan rana ban bi shi zuwa masallaci da wuri ba.
” A daidai ina alwala a gida sai naga mutane da gudun tsiya sun yo kaina, daga nan ne nima na bisu da gudun tsiya.
Waɗanda abin ya auku a idon su sun bayyana cewa maharan sun zagaye masallacin ne daga nan suka yi awon gaba da masallata, da na’ibi da ladan.
Akwai wanda ya yi kokarin arcewa Habibu Fada, amma ƴan bindigan sun harbe shi sai dai bai mutu ba, yanzu haka yana asibiti kwance.
Wani mazaunin garin Zugu ya bayyana cewa akalla mutum sama da 40 ne maharan suka arce da su.
Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin sai dai ta ce ba ta takamamman adadin yawan waɗanda aka sace.
Discussion about this post