Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ai tuni APC ta mutu. Wannan raddi na cikin martanin da Kakakin Yaɗa Labarai na PDP, Debo Ologunagba ya mayar wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu a ranar Lahadi.
A ranar Asabar ce dai Tinubu ya ragargaji PDP a wurin ƙaddamar da lambarin kamfen da kuma bargar motocin yaƙin neman zaɓen sa, wanda shugabannin majalisun dokoki na Arewa su ka shirya, a Abuja.
Bayan Tinubu ya gama bayyana yadda zai gano kuma na magance matsalolin Najeriya, ya yi amfani da damar da ya samu ya yi kaca-kaca da PDP.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatin da zai kafa idan ya ci zaɓen 2023, za ta ƙunshi zaƙaƙuran mutanen da za su yi hangen nesan gano matsalolin da ƙasar nan ke fama da su, tare da magance su nan da nan.
Tinubu ya yi wannan bayani a Abuja ranar Asabar, lokacin da aka ƙaddamar da motoci masu ɗauke da tambarin kamfen na Gida-gida, wato “Door-to-Door Tinubu/Shettima 2023”, wanda ƙungiyar Kakakin Majalisar Dokokin Jihohin Arewa na APC su ka shirya.
Tinubu ya ce sannan kuma tawagar sa na da hazaƙar azurta Najeriya da ‘yan ƙasa baki ɗaya.
“Ai mu ne masu hangen nesan cikin jam’iyya. Mu na son ilmi mai inganci ga ‘ya’yan mu, mu na buƙatar ci gaban Najeriya da arzikin ƙasa musamman ta hanyar bunƙasa harkokin noma ta hanyar dabarun zamani.
“Mu na ji da kan mu cewa za mu iya. Mu na da abin da ake buƙata wajen masu irin wannan ƙoƙari da kishi. Mu na da wannan ƙudiri. Kuma mu na da wannan juriyar iya yin aikin.” Inji Tinubu.
Ya ƙara da cewa APC ba ta damu da PDP ba, ballantana ma ta tsaya ta na ce-ce-ku-ce da ita ba.
Ya ce a matsayin APC na jam’iyyar da ta ƙunshi masu tunani, ba ta buƙatar ɓata lokacin yin hayaniya da PDP, jam’iyyar da rigimar shugabanci ma kaɗai ya ishe ta.
“Kada mu riƙa surfa wa jam’iyyun adawa zagi. Ai mun fi su sanin ya-kamata. Mun fi su basira da nagarta. Ta mu ba irin ta su ba ce.
“Sun yi shekaru 16 su na mulki, amma a lokacin sun manta cewa akwai buƙatar jiragen ƙasa masu jigilar jama’a da kayan su a ƙasar nan.” Inji Tinubu.
Daga nan ya shawarci PDP cewa ta jira ta ga irin kayarwar da APC za ta yi mata a ranar zaɓen shugaban ƙasa.
Haka kuma Tinubu ya gode wa ƙungiyar ‘yan Majalisar Dokokin Arewa dangane da wannan yunƙurin haɗa kayan kamfen da su ka fara yi masa.
“Kun sauƙaƙa mana rayuwa, saboda ko sisi ba ku nema a wurin mu ba. Lallai ku ma ku na neman ganin Najeriya ta zama ƙasaitacciyar ƙasa.
Shi ma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya ce idan aka zaɓi Tinubu, za su gina sabuwar Najeriya.
Raddin PDP Ga Tinubu:
PDP ta ce surutan da Tinubu ya riƙa yi wani yunƙuri ne na kaucewa daga batutuwan da su ne su ka kamata a tattauna a tattauna kan su, wato fannonin da gwamnatin APC ta gaza.
Ta ce surutan daTinubu ya riƙa yi sun nuna cewa a ruɗe ya ke, kuma ya gigita ganin irin tasirin da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar ke da shi a yanzu
“Ba kamar APC ba, jam’iyyar da ta mutu, ba sauran wani ƙarfi a jikin ta. PDP ce zata ceto ‘yan Najeriya da mulkin tsanani na APC.”
PDP ta ce a kullum Tinubu na kwana ya na tashi da fargabar rashin cancanta tsayawa takara, saboda ya na da matsalar yin ƙaryar shekaru, ƙaryar asali sai kuma zargin danne dukiyar jama’a da sauran zarge-zargen da su ka dabaibaye shi.
Tinubu Ne Gogarman Ƙarin Harajin Jiki-magayi, Kuɗin Lantarki Da Na Fetur -PDP:
Kakakin PDP ya ce ai Tinubu ne silar yi wa ‘yan Najeriya ƙarin kuɗin harajin-jiki-magayi (VAT), Kuɗin wutar lantarki, ƙarin farashin fetur da sauran harajin da gwamnatin APC ta lafta wa ‘yan Najeriya, maimakon samar masu sauƙin rayuwa.
Yayin da PDP ta bayyana Tinubu a matsayin rubabin da ya zama alaƙaƙai a cikin APC, ta ce shi ya sa a kullum ɗimbin jama’a ke fita daga APC su na shiga PDP.
PDP ta ce cikin wata ɗaya magoya bayan APC miliyan biyar sun koma PDP, yayin da a Jihar Legas inda Tinubu ke taƙama, mutum miliyan ɗaya ya fice daga APC zuws PDP.
Discussion about this post